Manyan Labarai A Yau
Majalisar dokoki a kasar Amurka ta yabawa gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma bisa irin kyakkaywan jagorancinsa, ta karrama shi da lambar yabo ta musamman.
Fadar shugaban kasa ta yi tsokaci kan batun ma'aikatar bogi da ake ta cece-kuce . Ta umarci hukumomin DSS da EFCC su gudanar da bincike kan lamarin
Babbar kotun jihar Kwara ta sanya ranar 22 ga Yulin 2026 domin gurfanar da Bukola Saraki kan zargin bata wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq suna da wallafa ƙarya.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da ta'annati da dukiyar kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana yadda 'yan Yahoo suka kwashe kudin wata mai shari'a.
Shahararriyar jarumar fim, Clarion Chukwurah, ta ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, shawara kan matsalar rashin tsaron da ake ci gaba da fuskanta a Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gaggauta bada umarnin gudanar da bincike kan hukumar PFIPC.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan ta'addan ISWAP suka kai a jihar Borno. Sojojin sun kashe 'yan ta'adda tare da kwato makamai.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Enduring Peace sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a Plateau. Sojojin sun kuma kwato makamai a hannunsu.
Mai ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, Adeniyi Adeyemi, ya yi zarge-zarge kan gwamnatin tarayya. Adeniyi ya ce gwamnati na kokarin rufe masa baki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari