Ana Shirin Sauya Dan Takarar Gwamnan PDP a Benue? Gaskiya Ta Fito

Ana Shirin Sauya Dan Takarar Gwamnan PDP a Benue? Gaskiya Ta Fito

  • Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, ya yi magana rahoton da ke cewa shugabannin PDP na shirin sauya ɗan takarar gwamnan jihar na 2027
  • Ortom ya ce taron da ya haɗa shi da Abba Moro, Michael Aondoakaa da wasu manyan ’ya’yan Benue na neman haɗin kan masu ruwa da tsaki ne
  • Tsohon gwamnan ya tabbatar da cewa manyan masu ruwa na iya tattaunawa domin duba muhimman batutuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Makurdi, Jihar Benue – Tsohon gwamnan jihar Benue kuma jagoran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar, Cif Samuel Ortom, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa za a sauya dan takarar gwamna na jam'iyyar.

Samuel Ortom karyata rahotannin da ke cewa shi da wasu shugabannin jam’iyyar na shirin sauya Cif Michael Aondoakaa, SAN, da Dr. Pius Akutah, sakataren zartarwa na Nigerian Shippers’ Council.

Kara karanta wannan

An ji dalilin Saudiyya da ta garkame wasu 'yan Najeriya a gidan yari

Ortom ya yi jawabai
Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom Hoto: Samuel Ortom
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Ortom ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai, Zege Terhide, ya fitar.

Ortom ya bayyana rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin “mugun shiri” da aka karkatar da gaskiyar wani taro da ya yi da wasu fitattun ’ya’yan Benue.

Ortom ya bayyana abin da ya faru

Tsohon gwamnan ya ce shi, tare da jagoran marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro, da ɗan takarar PDP na gwamna, Aondoakaa, sun gana da wasu fitattun ’ya’yan Benue.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Cif Simon Shango, Farfesa Iyorwuese Hagher, Dr. Pius Akutah, Emmanuel Ameh da Dr. Matthias Byuan.

A cewar Ortom, taron wani ɓangare ne na ci gaba da tuntubar juna da nufin gina babban ƙawancen dabaru tsakanin masu ruwa da tsaki na Benue domin amfanin jihar baki ɗaya.

Ya ce babu lokacin da aka tattauna, aka yi tunanin ko aka sanya batun sauya Aondoakaa a matsayin ɗan takarar PDP a cikin ajandar taron.

Kara karanta wannan

Halin da wasu ƴan Najeriya ke ciki a gidan gyaran hali na Saudiyya

“Babu lokacin da aka tattauna sauya Cif Aondoakaa a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP, ko aka yi tunanin hakan ko kuma aka sanya batun a cikin ajandar taron,” in ji Ortom.

Ortom ya soki rahoton

Tsohon gwamnan ya bayyana yunƙurin fassara taron da wata ma’ana dabam a matsayin wani shiri na ɓata suna, yana mai cewa tuntubar juna tsakanin ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban abu ne na yau da kullum a tsarin dimokuraɗiyya.

“Saboda haka, mugun shiri ne mutum ya ɗauki sahihin taron shugabannin Benue ya ƙirƙiro masa wata manufa ta daban kwata-kwata,” in ji shi.

Ortom ya jaddada cewa bai kamata a riƙa kallon tuntuba da ganawa tsakanin ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki a matsayin wata boyayyar makarkashiya ba, musamman idan manufar irin waɗannan ganawarsu ita ce kare babban muradin jama’a.

Aondoakaa ne ɗan takarar PDP

Tsohon gwamnan ya kuma kawo ƙarshen jita-jitar da ke kan tikitin PDP na gwamna, inda ya bayyana babu shakka cewa Aondoakaa na nan a matsayin ɗan takarar da jam’iyyar ta tsayar domin zaɓen gwamnan Benue na 2027.

“Cif Michael Aondoakaa, SAN, shi ne halastaccen ɗan takarar PDP na kujerar gwamnan jihar Benue a zaɓen 2027,” in ji Ortom.

Kara karanta wannan

Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Ya ce tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma tsohon ministan shari’a na da cikakken amincewa da goyon bayan shugabannin PDP da mambobin jam’iyyar a faɗin jihar.

An yi magana kan dan takarar gwamnan PDP a Benue
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

PDP ta rasa jiga-jigai a Gombe

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) guda biyu a jihar Gombe sun yi murabus daga jam’iyyar.

Tsohon shugaban karamar hukumar Funakaye kuma tsohon shugaban PDP a karamar hukumar, Hon. Alhaji Ibrahim Yusuf, da mataimakin sakataren jam’iyyar a jihar Gombe, Hon. Mohammed Babani Bajoga, sun sanar da murabus dinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com