Sakon Abba ga Malamai, Sarakuna da Gwamnonin da Suka Halarci Auren Gata a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sako ga sarakunan gargajiya da malaman addini bisa irin gudunmawar da suka bayar
- A ranar Asabar 8 ga watan Agusta, 2026 ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi shagalin bikin auren mutane 3,000 a birnin jihar
- Gwamnan ya kuma tura sako ga angwaye da amare da suka rabauta da shiga wannan tsari ganin za su fara sabuwar rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna godiyarsa ga sarakunan gargajiya, malaman addinin Musulunci, gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da sauran manyan baki.
Ya ce sun yi namijin kokari wajen bayar gudunmawar wajen ganin an gudanar da shirin auren ma’aurata 3,000 jihar cikin nasara ba tare da matsala ba.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 8 ga watan Agustan 2026, ya kuma wallafa a shafin Facebook.
Gwamnan Kano ya godewa na
Gwamnan ya bayyana godiya ta musamman ga shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano da sarakunan Kano, Rano, Karaye da Gaya, bisa shawarwarin da suka bayar, addu’o’in da gudunmawar da suka bayar wajen ganin bikin ya yi nasara.
Ya ce rawar da sarakunan suka taka, musamman wajen ba da shawarwari da addu’a, ta taimaka matuka wajen samun nasarar shirin.
Gwamnan ya kuma gode wa malaman addinin Musulunci da suka zo daga sassa daban-daban na Najeriya domin halartar bikin.
Shawarar Gwamna Abba ga ma'aurata
Gwamnan ha bayyana cewa addu’o’i da shawarwarin malaman sun kasance muhimmin ginshiki wajen samun nasarar shirin auren ma’auratan.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya yaba wa takwarorinsa na jihohin Arewa maso Yamma, ciki har da Gwamnan Katsina, Umar Dikko Radda.
Sai kuma Gwamnan Jigawa, Umar Namadi; da Gwamnan Kebbi, Dr Nasir Idris, tare da wakilansu, bisa girmama bikin da kuma halartar wannan muhimmin taro.

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma bayyana godiyarsa ga shugabanni da ma’aikatan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano karkashin jagorancin Kwamandan-Janar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Abba Kabir Yusuf ya kara da yi wa ma'auratan nasiha da su zauna lafiya da juna tare da hakuri domin a samun nasarar da aka sanya a gaba.
An kashe N10.5bn a auren Kano
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta kashe sama da N1.5 biliyan wajen shirin Auren Gata na 2026.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an yi wa dukkan ma’auratan gwaje-gwajen lafiya, shawarwarin aure da horo kafin shigar da su cikin shirin da aka dade ana masa tanadi.
Kowace amarya ta samu N100,000 na sadaki da karin N100,000 a matsayin tallafin jari, baya ga kayan daki da abinci domin ya tallafa masu a farkon amarci.
Asali: Legit.ng

