Majalisa Ta Cimma Matsaya kan Bukatar Tinubu Ta Runtumo Bashin $515.m

Majalisa Ta Cimma Matsaya kan Bukatar Tinubu Ta Runtumo Bashin $515.m

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da bukatarsa ga majalisa, inda ya nemi ta sahale masa ya sake karbo bashi
  • Majalisar wakilai ta yi zama inda ta amince da bukatar shugaban kasar ta runtumo bashin $516.3m daga kasar Jamus
  • Sai dai, majalisar ta dauki wasu matakai domin ganin cewa an yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace domin su amfani 'yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta cimma matsaya kan bukatar shugaban kasa Bola Tinubu ta neman amincewarta ya ciyo bashin $516.3m.

Majalisar wakilan ta amince a karbo bashin &516.3m daga bankin Deutsche Bank AG domin samar da kuɗaɗen gina sashe na 1 (bangare na 1A da 1B) na aikin babban titin Sokoto zuwa Badagry.

Majalisa ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubh
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen Hoto: @aonanuga1956, @HouseNGR
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa majalisar ta amince da bukatar ne yayin zamanta na ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Fintiri zai fafata da babban dan kasuwa kan kujerar sanata a zaben 2027

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu

Amincewar ta biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan tallafi, rance da sarrafa bashi yayin zaman majalisar, jaridar TheCable ta kawo rahoton.

Yayin da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin, Abubakar Hassan Nalaraba, ya buƙaci ’yan majalisar da su amince da buƙatar neman kuɗaɗen domin gina sashen hanyar mai tsawon kilomita 120.

Tun da farko, wani mamba a kwamitin, Abdullahi El-Rashid, wanda ke wakiltar mazaɓar tarayya ta Dukku/Nafada a jihar Gombe, ya gabatar da kudirin duba rahoton, inda ya jaddada muhimmancin hanyar ga haɗin kan tattalin arziƙin ƙasa.

Bello Isah Ambarura, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Illela/Gwadabawa a jihar Sokoto, ne ya marawa kudirin baya.

’Yan majalisar sun amince da dukkan shawarwari guda biyar, ciki har da tsarin bashin da kuma sanya shi a cikin tsarin rance na gwamnatin tarayya.

'Yan majalisa sun dauki matakai

A matsayin matakan tabbatar da gaskiya, majalisar ta ba da umarnin sa ido sosai, ciki har da rahotannin kowane bayan watanni uku daga ma’aikatar kuɗi ta harayya, ofishin kula da bashi (DMO), da ma’aikatar ayyuka ta tarayya kan yadda ake gudanar da aikin da kuma yadda ake fitar da kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

Bayan na Pantami, an tara wa dan majalisar tarayya miliyoyi domin takara

Haka kuma ’yan majalisar sun bayar da umarnin cewa a gabatar da duk yarjejeniyoyin samar da kuɗaɗen da aka sanya wa hannu ga majalisar cikin kwanaki 30 da kammala yarjejeniyar, tare da ci gaba da sanya ido daga kwamitocin da abin ya shafa.

Tinubu ya nemi bukata wajen majalisa

Wannan amincewa ta biyo bayan buƙatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tun farko, wanda a watan Afrilun 2026 ya rubutawa majalisar dokoki ta kasa wasiƙar neman amincewa da ciyo bashin na ƙasashen waje.

Majalisa ta amince da bukatar Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

A cikin buƙatar, Shugaban ya bayyana cewa bashin zai samar da kuɗaɗen gina sashe na 1, bangaren 1A da 1B na babban titin, wanda yake wani ɓangare ne na hanyar.

Hanyar wadda ta kai kilomita 1,000 za ta haɗa yankin Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, tun daga Sokoto za ta ratsa cikin jihohin Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, da Ogun har zuwa Badagry da ke Legas.

'Yan majalisar wakilan NNPP sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan majalisar wakilan Najeriya na jam'iyyar NNPP daga jihar Kano sun sanar da ficewa daga jam'iyyar.

Mambobin majalisar wakilan ta Najeriya guda hudu sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar ADC bayan ficewa daga NNPP.

'Yan majalisar wakilan sun bayyana rikicin cikin gida a tsofaffin jam’iyyunsu a matsayin dalilin sauya shekar tasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng