Malami da Sowore Sun Yi Musayar Zafafan Kalamai a Harabar Kotu, An Tuna Lokacin Mulkin Buhari
- Tsohon Antoni Janar/Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya hadu da fitaccen dan gwagwramayar nan, Omoyele Sowore a kotu a Abuja
- Malami da Sowore sun yi musayar yawu a tsakaninsu musamman kan batun shari'ar cin hanci da tsohon ministan ke fuskanta
- Sowore ya zolayi Malami a harabar kotu, tare da yi masa tayin shiga tawagarsa ta yan fafutukar neman yanci don gyara tsarin shari'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Antoni Janar na tarayya, Abubakar Malami (SAN) da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, sun yi musayar yawu a harabar kotu a Abuja.
Bayanai sun nuna cewa Sowore ne ya fara zolayar Malami kan shari’ar cin hanci da rashawa da yake fuskanta, yana mai cewa maiamin da ya yi amfani da shi a baya yanzu ya fada kansa.

Source: Facebook
Malami da Sawore sun yi musayar yawu
Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne a harabar kotu a Abuja, inda Sowore ya tunkari Malami kafin fara zaman shari’ar da Hukumar EFCC ta shigar kansa kan tuhume-tuhume 16 na zargin halasta kudin haram.
Sowore ya tunatar da Malami yadda aka gurfanar da shi a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana mai cewa yanzu Malami na fuskantar irin wannan yanayi.
“Yanzu ka ga yadda ake ji idan ana muzgunawa mutum. Lokacin da kake tare da Buhari kana takama, mun gargade ka cewa tsarin shari’a na da matsala amma ba ka saurara ba, yanzu ga shi yana aiki a kanka,” in ji Sowore.
Yunkurin jawo Malami cikin tafiyarsa
Sowore ya kuma yi ƙoƙarin ba Malami hular ‘Revolution Now’, yana mai cewa ya kamata ya shiga tafiyarsa domin gyara tsarin.
“Mu ba shi hular 'yan gwagwarmaya, yanzu ka gane tsarin ya lalace, mu na so ka shigo ka hada kai da mu,” in ji shi.
Malami ya maida martani ga Sowore
Sai dai tsohon ministan na shari'a, Abubakar Malami ya ƙi karɓar hular, yana mai cewa, “nima ina da tawa hular."
Malami ya kuma tanka wa Sowore lokacin da ya fada masa cewa a yanzu reshe ya juye da mujiya, ana ladabtar da shi da shari'ar da ya rika takama da ita, yana mai cewa halin da yake ciki ba ya nufin an kai shi kasa ba ne.

Source: Facebook
Wannan cacar baki ta samo asali tun shekarar 2019, lokacin da aka kama Sowore kan gangamin ‘Revolution Now’ tare da tuhume-tuhume da suka haɗa da cin amanar ƙasa.
A yayin musayar yawun da suka yi, Sowore ya tambayi Malami ko har yanzu yana iya halartar tarukan jam’iyyar ADC, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Malami ya amsa cewa yana halarta, duk da cewa bai samu damar halartar taron Ibadan ba, yana mai cewa har yanzu yana cikin harkokin siyasa.
Sowore ya tunkari Ministan Tinubu a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen mai fafutukar kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore, ya tunkari Ministan Ayyuka, David Umahi, a hedkwatar ‘yan sanda ta Abuja.
Yayin da suka hadu a hadu a hedkwatar ‘yan sandan Abuja, Sowore ya zargi Ministan da amfani da karfin iko wajen zaluntar wata mata mai suna TracyNither Nicolas Ohiri.
Ma’aikatan Ministan sun yi yi kokarin ture Sowore, amma dan gwagwarmayar ya tsaya da kafarsa tare da zargin ministan da yin karfa-karfa
Asali: Legit.ng


