Malamin Addini Ya Yi Hasashen Gwamnoni 5 da Za Su Fadi a Zaben 2027
- Primate Babatunde Elijah Ayodele ya yi hasashen matsala ga wasu gwamnoni bayan babban zaɓen 2027
- Hukumar INEC, kwanan nan ta sake tura ranar zaɓen gwamnoni na 2027 a jihohin Najeriya da dama zuwa ranar 6 ga Fabrairun 2027
- Wani mai ruwa da tsaki a harkar siyasa, Mike Igini, ya buƙaci ’yan adawa da su matsa lamba don yi wa sassan dokar zaɓe mai cike da kace-nace garambawul
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kano, jihar Kano - Gabanin zaɓen 2027, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan makomar wasu gwamnoni.
Primate Ayodele ya bayyana cewa ‘ba kowane gwamna a Najeriya ba ne zai yi farin ciki bayan zaɓen 2027’.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu kuma aka aika wa jaridar Legit.ng.
Wane hasashe Ayodele ya yi kan gwamnonin APC?
Primate Ayodele ya ambaci wasu daga cikin jihohin da ya yi iƙirarin cewa za su fuskanci hakan.
“Ba kowane gwamna ba ne zai yi murmushi bayan zaɓen. Jihohin da abin zai shafa su ne Rivers, Akwa Ibom, Sokoto, Kano, da Kaduna.” inji shi
Dukkan jihohin da Primate Ayodele ya ambata a halin yanzu ana mulkar su ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki.
Jihohin da aka bayyana su ne:
- Kano (Gwamna Abba Kabir Yusuf)
- Kaduna (Gwamna Uba Sani)
- Rivers (Gwamna Siminalayi Fubara)
- Akwa Ibom (Gwamna Umo Eno)
- Sokoto (Gwamna Ahmad Aliyu)
Yaushe ne zaɓen gwamnoni na 2027?
Legit Hausa ta tuna cewa a watan Fabrairun 2026, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sauya da ranakun babban zaɓen 2027 biyo bayan kafa sabuwar dokar zaɓe.
INEC ta bayyana cewa za a gudanar zaɓen majalisun dokoki na jihohi da na gwamnoni a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2027.
Tun farko an tsayar da zaɓubbukan ne a ranar 6 ga Maris, 2027, a ƙarƙashin dokar zaɓe ta 2022 da aka soke.

Source: Facebook
Igini ya buƙaci garambawul ga dokar zaɓe
A halin da ake ciki kuma, Mike Igini, tsohon Kwamishinan zaɓe na INEC, ya buƙaci jam’iyyun siyasa na adawa da su gaggauta neman gyara ga sassa masu cike da kace-nace a cikin dokar aɓe ta 2026 gabanin babban zaɓen 2027.
A cewar jaridar Premium Times a wani rahoto na ranar Litinin, 27 ga Afrilu, Igini ya yi wannan kiran ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a taron jam’iyyun adawa da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo, ranar 25 ga Afrilun 2026.
An samu wanda zai yi takara da Tinubu a APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Francis Osifo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawar shugaban kasa a zaben 2027.
Stanley Osifo ya bayyana cewa zai fafata da Shugaba Bola Tinubu don neman tikitin jam'iyyar na APC na takarar shugaban kasa.
Osifo ya sanar da shirinsa na sayen fom ɗin tsayawa takara na jam’iyyar APC kan kuɗi Naira miliyan 100.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

