‘Kowane Uba Zai Yi Alfahari da Samun ɗa Kamar Seyi’: An Gwaɗa Yaron Tinubu

‘Kowane Uba Zai Yi Alfahari da Samun ɗa Kamar Seyi’: An Gwaɗa Yaron Tinubu

  • Segun Showunmi, tsohon kakakin Atiku Abubakar, ya bayyana Seyi Tinubu a matsayin ɗa abin koyi
  • Showunmi ya ce abin da ya burge shi a City Boy Movement shi ne haɗin kan matasa daga kabilu, addinai da al’ummomi daban-daban
  • Ya yaba wa Seyi saboda tawali’u, girmama ma’aikata da ƙoƙarin haɗa kan ‘yan Najeriya, yana cewa ayyukansa na da matukar amfani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon kakakin Atiku Abubakar, Segun Showunmi ya yi magana game da halayen kirki na dan shugaban kasa, Bola Tinubu.

Sowunmi ya bayyana Seyi Tinubu a matsayin “ɗa abin yabawa”, yana cewa kowane uba zai yi godiya samun ɗa irinsa.

An yabawa halayen Seyi Tinubu
Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu. Hoto: Seyi Tinubu.
Source: Twitter

Showunmi, wanda ya shirya ƙungiyar The Alternative, ya ce kwanan nan ya ziyarci ofishin City Boy Movement, inda Seyi da kansa ya zagaya da shi wurin, kamar yadda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Wuta ta yi wuta: Babban sojan Amurka na neman a fita a yaki da Iran

Abin da ya burge Sowunmi game da Tinubu

Dan siyasar ya ce abin da ya burge shi ba tsarin ginin ofishin ba ne, sai dai al’adun haɗin kai da suka haɗa matasan Najeriya daban-daban.

Ya ce:

“Babu wani uba da zai samu ɗa kamar Seyi Tinubu, ba tare da ya yi matuƙar godiya ga Allah Maɗaukaki ba.”

Showunmi ya ce ya ji daɗi sosai saboda yadda Seyi ke aiki tuƙuru domin tabbatar da amincewar da aka yi masa, tare da samun matsayinsa ta ƙoƙari da jajircewa.

Ya bayyana cewa City Boy Movement na nuna shugabanci mai tsari, yana mai cewa ƙungiyar tana ba maza da mata dama daidai, tare da haɗa masu nakasa.

Ya ce yadda Seyi ke mu’amala da mutanen da ke aiki tare da shi ya yi masa matuƙar tasiri, musamman yadda yake nuna musu girmamawa.

Showunmi ya ce:

“Abin da ya fi ɗaukar hankalina ba tsarin wurin ba ne, sai dai al’adar aiki. Na ga Seyi yana mu’amala da tawagarsa.”

Kara karanta wannan

An ji dalilin Saudiyya da ta garkame wasu 'yan Najeriya a gidan yari

Ya ƙara da cewa ya ga Seyi yana raba kayan ciye-ciye da ma’aikatan da ke bayan fage, ba tare da nuna isa ko fifiko a kansu ba.

A cewarsa, babu wani yanayi na girman kai ko nisantar ma’aikata, domin girmamawa tana gudana cikin sauƙi, yayin da ma’aikatan ke jin ana daraja su.

Sowunmi ya yabawa Seyi Tinubu
Tsohon na kusa da Atiku Abubakar, Segun Sowunmi da Bola Tinubu. Hoto: Segun Sowunmi.
Source: Facebook

Kokarin da Seyi Tinubu ke yi

Showunmi ya bayyana cewa ƙoƙarin da Seyi ke yi a yanzu zai haifar da amfani nan gaba, musamman wajen gina gadoji tsakanin sassa daban-daban na Najeriya.

Ya ce ayyukan Seyi na iya taimakawa sosai wajen cimma manufar siyasar da yake goyon baya, tare da nuna cewa shiga siyasa na iya kasancewa cikin tsari da haɗin kai.

Ya ƙara da cewa kowace ƙasa na buƙatar matasa masu son haɗa mutane wuri guda, aiki tuƙuru da hidima cikin tawali’u.

Showunmi ya ce:

“Kowane uba yana son ɗa da zai ƙara daraja ga gadonsa. Kowace ƙasa kuma tana buƙatar matasa masu aiki da haɗa mutane.”

A cewarsa, daga abin da ya gani, Seyi Tinubu yana ƙoƙarin zama irin wannan mutum mai kishin aiki da haɗin kan jama’a.

Kara karanta wannan

Halin da wasu ƴan Najeriya ke ciki a gidan gyaran hali na Saudiyya

Seyi Tinubu ya saba wa wasu matasan Arewa

Mun ba ku labarin cewa wata kungiyar matasan Arewa ta yi barazanar janye goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 kan abin da ɗansa ya yi.

Kungiyar ta zargi Seyi Tinubu da fifita matasan Yarabawa wajen nade-nade da shugabancin kungiyoyin matasa.

Ta ce shugabannin kungiyoyin goyon bayan APC 1,378 a Arewa za su fara tuntuba da nazari kan matakin da za su dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.