Abubakar Malami Ya Yi Zarge Zarge kan EFCC a gaban Kotu, Ya Kafa Hujjoji
- Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, na fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotu wadanda hukumar EFCC ta shigar a kansa
- A baya dai kotu ta ba da umarnin kwace wasu daga cikin kadarorinsa na dan lokaci kamar yadda jami'an EFCC suka bukata
- Abubakar Malami ya kalubalanci matakin inda ya zargi hukumar da fadin abin da yake ba daidai ba don ganin an kwace kadarorin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi zarge-zarge kan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Abubakar Malami ya zargi hukumar EFCC da ƙara gishiri kan darajar kadarorinsa domin yaudarar kotu da kuma samun umarnin ƙwace su na ɗan lokaci.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce tsohon Ministan ya bayyana hakan ne yayin zaman kotu na ranar Litinin, 27 ga watan Afirilun 2026.
Kotu ta umarci kwace kadarorin Abubakar Malami
A ranar 6 ga Janairu, Emeka Nwite, alƙalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ba da umarnin ƙwace kadarori 57 na Malami na lokacin wucin-gadi, waɗanda ake zargin an same su ne ta hanyar ayyukan haram.
A cewar hukumar EFCC, darajar kadarorin na tsohon Ministan shari'ar ta kai N213,234,120,000.
Abubakar Malami ya karyata hukumar EFCC
Sai dai, a cikin wata takardar da ya gabatar a gaban kotu ranar Litinin, tsohon Ministan ya ce hukumar yaƙi da cin hancin ta dogara ne kan karawa gishiri miya kan darajar kadarorin.
“An samu umarnin ƙwace kadarorin ne ta hanyar ƙarin gishiri a fili, sanya darajar ƙarya cikin ƙeta, da kuma ƙididdigar darajar da ba ta dace ba wadda aka karkata ta da gangan domin yaudarar wannan babbar kotu."
- Abubakar Malami
Abubakar Malami ya ba da misalai
Tsohon babban lauyan gwamnatin ya kawo misalai da dama inda ya yi iƙirarin cewa lissafin EFCC ya ninka farashin da aka saya ko kuma ƙididdigar masu zaman kansu sau da yawa.

Kara karanta wannan
Malami da Sowore sun yi musayar zafafan kalamai a harabar Kotu, an tuna lokacin mulkin Buhari
Ya ce wani babban gida a Maitama, Abuja, wanda aka saya kan Naira miliyan 500, EFCC ta sanya masa darajar Naira biliyan 5.95.
Haka kuma, ya ce babban filin Jami’ar Rayhaan wanda aka saya kan Naira miliyan 150, hukumar EFCC ta sanya masa darajar Naira biliyan 56.
Har ila yau, ya ƙalubalanci lissafin wurin jami’ar na ɗan lokaci, wanda ya ce an saya kan Naira miliyan 400 amma EFCC ta kiyasta shi a kan naira biliyan 37.8.
Malami ya ce wata ƙididdiga mai zaman kanta da kamfanin gine-gine na Jide Taiwo & Co ya yi ta nuna darajar kadarorin kasa da waɗanda EFCC ta gabatar.

Source: Twitter
Malami ya ce EFCC ta kasa ba da hujja
Tsohon ministan ya kuma bayyana cewa EFCC ta kasa kafa wata alaƙa tsakanin kadarorin da ayyukan laifi, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Ya ƙara da cewa hukumar ba ta gabatar da wata takarda da ke nuna cewa an sayi kadarorin ne da kuɗaɗen aikata laifi ko kuɗaɗen da ke na gwamnatin tarayya ba.
Malami ya ce ya bayyana kadarorin nasa a cikin takardun da ya kai wa hukumar kula da da'ar ma’aikata (CCB) a shekaru daban-daban, ciki har da 2015, 2019, da 2023.

Kara karanta wannan
Jami'ai sun kai wa Trump da matarsa dauki bayan ɗan bindiga ya kai hari taron White House
Tsohon babban lauyan gwamnatin yana roƙon kotun da ta soke umarnin ƙwace kadarorin, inda ya bayyana cewa an ba da umarnin ne bisa zato maimakon hujja.
Gwamnati ta sauya tuhume-tuhume kan Malami
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi gyara a tuhume-tuhumen da take yi wa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami.
Gwamnatin ta cire zargin da ya shafi ɗaukar nauyin ta’addanci da take yi a baya kan tsohon Ministan na shari'a a zamanin Muhammadu Buhari.
A cikin tuhumar da aka gyara, masu shigar da ƙara suna zargin cewa an samu makamai da harsasai a gidan Abubakar Malami da ke Birnin Kebbi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
