Magana Ta Fito: Peter Obi Ya Bayyana Dalilin Ganawa da Jonathan
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya kai ziyara ga Goodluck Ebele Jonathan, wanda ya taba mulkin Najeriya
- Peter Obi ya ziyarci Goodluck Jonathan ne tare da tawagarsa wadda ta kunshi jiga-jigan 'yan siyasa daga yankin Kudu maso Gabas
- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bayyana abin da suka tattauna da Jonathan yayin ziyarar da suka kai masa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya yi magana kan ganawar da ya yi da Goodluck Ebele Jonathan.
Peter Obi ya bayyana ganawar sirrin da ya yi da tsohon shugaban kasar a matsayin mai ma'ana, inda ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan makomar Najeriya.

Source: Twitter
Peter Obi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Asabar, 27 ga watan Afirilun 2026.
Me Peter Obi ya tattauna da Goodluck Jonathan?
Obi, wanda ya jagoranci tawagar fitattun shugabannin Kudu maso Gabas zuwa gidan Jonathan, ya ce wannan ziyarar tana daga cikin tuntubar juna da yake ci gaba da yi da masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen 2027.
"Tattaunawarmu ta kasance ta gaskiya, mai cike da tunani, kuma ta ginu ne kan buƙatar gaggawa ta mayar da Najeriya kan turbar haɗin kai, tsaro, kwanciyar hankali, samar da shugabanci na kowa da kowa.”
- Peter Obi
Ya lura cewa ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu sun sa ya zama dole shugabanni su yi aiki tare ba tare da la’akari da iyakokin shiyya ba.
“A daidai lokacin da ƙasarmu ke ci gaba da kokawa da mawuyacin halin tattalin arziki, ƙaruwar rashin tsaro, da zurfafan rarrabuwar kawuna a cikin al’umma, ya zama wajibi shugabanni daga sassa daban-daban su haɗu don yin tunani, tuntuba, da kuma ɗaukar mataki don maslahar al’ummar Najeriya baki ɗaya."
- Peter Obi
Peter Obi ya magantu kan shugabanci
Obi ya jaddada cewa irin shugabancin da Najeriya ke buƙata ya kamata ya ba wa cancanta da hidima muhimmanci fiye da burin kashin kai.
“Najeriya a yau tana buƙatar shugabanci wanda ba burin kashin kai ke jagoranta ba, face ƙwarewa, hali na gari, iyawa, da tausayi. Shugabanci ba batun raba abin da ya rage ba ne, face ƙirƙirar abin da ake buƙata ne."
- Peter Obi
Ya ƙara nanata buƙatar sauya fasalin tattalin arziƙin ƙasar, inda ya ba da shawarar sauyawa daga cinye abubuwa zuwa samar da su ta hanyar amfani da albarkatun ɗan adam da na ƙasa don ci gaba gaba ɗaya.

Source: Twitter
Me Peter Obi ya ce kan zaben 2027?
Yayin da yake duban babban zaɓe mai zuwa, Obi ya bayyana zaɓukan 2027 a matsayin wani muhimmin lokaci ga ƙasar.
“Kada a kalli zaɓen 2027 a matsayin wani taron siyasa kawai, ya kamata a kalle shi a matsayin wata muhimmiyar dama ta sake daidaita alkiblar ƙasarmu."
“Dole ne ya shafi ɗan Najeriya wanda ya cancanci ingantaccen ilimi, ɗan kasuwar da ke gwagwarmaya wanda ke buƙatar yanayi mai kyau don haɓaka, da kuma miliyoyin ’yan ƙasa waɗanda kawai su ke sha’awar samun ƙasa mai tsaro da ayyuka na gari."
- Peter Obi
An kafa kungiyar Obi da Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa an kafa sabuwar kungiyar siyasa domin tafiyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi.
Magoya bayan tsofaffin gwamnonin biyu sun kafa kungiyar siyasa ƙungiyar siyasa mai suna Obi-Kwankwaso (OK) Movement.
An kafa kungiyar ne yayin da ake ƙara kulla ƙawancen siyasa gabanin zaɓen tsaida gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC don babban zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


