Hajj Mabrur: NAHCON Ta Sanya Lokacin Fara Jigilar Maniyyata
- Hukumar jin dadin Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kammala shirye-shiryen fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki
- NAHCON ta sanar da cewa za ta fara jigilar maniyyata zuwa Saudiyya domin Hajjin bana a farkon watan Mayun shekarar 2026
- A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar ta bayyana tsarin da za ta yi amfani da shi wajen jigilar maniyyatan da za su sauke farali a Saudiyya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar jin dadin Alhazzai ta kasa (NAHCON) ta sanar da lokacin fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa za a fara jigilar maniyyata zuwa aikin Hajjin bana a ranar 3 ga watan Mayun 2026.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a shafin X a ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan
Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48
A ina jirgin farko zai tashi?
Sanarwar ta bayyana cewa jirgin farko zai tashi ne daga filin jirgin sama na Gateway International Airport da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, ta hanyar amfani da jirgin FlyNas.
Sanarwar ta ce wannan ne karon farko da maniyyatan jihar Ogun za su tashi daga babban birnin jihar tun bayan gina filin jirgin.
"Sauran jiragen da za su tashi a wannan rana sun haɗa da Umza da Max Air daga Abuja tare da maniyyatan jihohin Kogi da Nasarawa, sai Air Peace daga Legas tare da maniyyatan jihar Oyo, yayin da wani jirgin FlyNas ɗin zai tashi daga Birnin Kebbi.”
- Fatima Sanda Usara
Ma'aikatan NAHCON sun tafi Saudiyya
Sai dai ta bayyana cewa ma’aikatan NAHCON, tare da mambobin rukunin jami’an lafiya na ƙasa, sun riga sun tashi a yau Talata, 28 ga Afrilun 2026, domin shirya karɓar maniyyatan Najeriya.
"NAHCON tana shawartar maniyyata da su sani cewa kowane kamfanin jirgi zai gudanar da jigilar ne shiyya-shiyya. Da zarar an kammala jigila daga wata shiyya aka koma ta gaba, kamfanin jirgin ba zai sake komawa waccan shiyyar ba."
"Maniyyacin da ya rasa jirginsa a shiyyarsa zai ɗauki nauyin bin jirgi a shiyya ta gaba. Sauran matsalolin sun haɗa da jiran sai an sake tsara su kafin samun damar tafiya."
“Abu na biyu, ku sani cewa dole ne maniyyata su yi tafiya ƙarƙashin rukuninsu na mutum 45, waɗanda katin 'Nusuk' ɗinsu zai kasance a shirye yana jiran isarsu a ƙasar Saudiyya."
"Don haka, ana shawartar kowane maniyyaci da ya tabbatar tare da sanin mambobin rukuninsa kafin tafiya.”
- Fatima Sanda Usara

Source: Twitter
Wace shawara aka ba maniyyata?
Ta shawarci maniyyata da su nemi lambobin wayar shugabannin rukuninsu da kuma jami’an jiha da za su yi tafiya tare da su a jirgi.
“Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya tabbatar wa maniyyatan Najeriya cewa hukumar ta kammala duk shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin 2026 cikin nasara da kwanciyar hankali.”
- Fatima Sanda Usara
Tinubu ya nada sabon shugaban NAHCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaba a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) bayan Farfesa Abdullahi Sale Usman ya yi murabus.

Kara karanta wannan
Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027
Fadar shugaban kasa ta bayyana ce Bola Tinubu ya nada Ismail Abba Yusuf a matsayin wanda zai jagoranci hukumar bayan murabus din Farfesa Abdullahi Sale Usman.
Rahotanni sun nuna cewa ya riƙe muƙamin Jakadan na musamman na Najeriya a Türkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.
Asali: Legit.ng
