Dan Takarar Gwamna Ya Watsar da Jam'iyyarsa, Ya Marawa APC baya a Zaben Jihar Osun

Dan Takarar Gwamna Ya Watsar da Jam'iyyarsa, Ya Marawa APC baya a Zaben Jihar Osun

  • Ɗan takarar APGA, Adesina Adeyemi-Doro, ya janye daga takarar gwamnan Osun tare da bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji
  • Adeyemi-Doro ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar shugabanni da mambobin jam’iyyar APGA a faɗin jihar
  • Janyewar tasa ta zo ne saura kusan mako guda a gudanar da zaɓen gwamnan Osun na 15 ga Agusta, inda gwamna mai ci, Ademola Adeleke, ke neman sake komawa kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Osun – Takarar gwamnan Jihar Osun ta ƙara samun sauyi yayin da ɗan takarar APGA, Adesina Adeyemi-Doro, ya janye daga takarar tare da bayyana goyon bayansa ga ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji.

Adeyemi-Doro ya bayyana matsayinsa ne a ranar Asabar yayin wani taro mai taken ‘Osun Youth Interactive Session with Oyebamiji’, wanda kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya shirya a Osogbo.

Kara karanta wannan

PDP ta goyi bayan gwamnan Kebbi da ke APC domin tazarce a 2027? Gaskiya ta fito

Dan takarar APGA a Osun ya janye ya barwa dan takarar APC
Dan takarar gwamna a APGA, Adesina Adeyemi-Doro da 'dan takarar APC, Bola Oyebamiji na zaben Osun. Hoto: @ConceptsJa67941/@RealFikayomi66
Source: Twitter

Ya ce ya yanke shawarar janyewa ne bayan gudanar da shawarwari da shugabannin jam’iyyarsa da kuma mambobin APGA a faɗin jihar, Premium Times.

A cewarsa, shawarwarin sun haifar da matsaya ɗaya ta goyon bayan takarar Oyebamiji, yana mai bayyana matakin a matsayin haɗin kai tsakanin masu kishin ci gaba.

Dalilin janyewar dan takarar APGA

Adeyemi-Doro ya ce ya shafe lokaci yana nazarin ’yan takarar da ke neman kujerar gwamnan Osun, kafin ya yanke shawarar mara wa Oyebamiji baya.

Ya ce ya tuntubi shugaban APGA na jihar, sakataren jam’iyyar da sauran manyan jami’an jam’iyyar kafin cimma matsayar haɗin kai.

Ya ce:

“Na zo nan ne a yau domin bayyana wa al’ummar Jihar Osun mubaya’armu, goyon bayanmu da haɗin kanmu yayin da muke shiga tare da Mai Girma Asiwaju Bola Oyebamiji da jam’iyyar APC.”

Ya ƙara da cewa:

“Na shafe lokaci ina kallon ’yan takarar sosai, kuma bayan tuntubar shugaban jam’iyyarmu na jihar, sakataren jam’iyyar da sauran manyan mambobi, mun cimma matsayar haɗin kai. A ƙarshe, dukkanmu masu kishin ci gaba ne.”

Kara karanta wannan

An kashe mutane 18 ana saura kwana 6 zaben gwamna, APC ta rasa mambobi 10

Adeyemi-Doro ya ce manufar haɗin kan ita ce taimaka wa Oyebamiji wajen samun nasarar zama gwamnan Osun a zaɓen da ke tafe.

Ya ce suna fatan za su yi aiki tare domin ganin an miƙa mulkin jihar ga Oyebamiji.

Oyebamiji ya karɓi goyon bayan

Bola Oyebamiji ya yi maraba da matakin Adeyemi-Doro, yana mai cewa ya yaba da goyon bayan da ɗan takarar APGA ya bayyana masa.

Ya kuma ce yaƙin neman zaɓensa zai ci gaba da neman goyon bayan ’yan takara da ƙungiyoyin siyasa da ba sa cikin APC domin ƙara faɗaɗa haɗin kan da za su shiga da shi cikin zaɓen.

Oyebamiji ya ce:

“Na gode sosai. Ina matuƙar godiya da wannan, kuma ina tabbatar muku cewa za mu yi aiki tare domin ceto Jihar Osun daga gwamnatin da ba ta yi abin da ya dace a halin yanzu ba.”

Channels TV ta rahoto cewa ya kuma yi alƙawarin cewa za a kula da mutanen da suka goyi bayansa.

APC na neman ƙarin jam’iyyu

Oyebamiji ya ce janyewar Adeyemi-Doro da goyon bayan da ya ba shi wani mataki ne da zai taimaka wajen faɗaɗa haɗin kan siyasa gabanin zaɓen.

Kara karanta wannan

Biliyoyi sun ƙaru': Gwamna a Arewa yana jin dadin kudin cire tallafi a jiharsa

Ya bayyana cewa kamfen ɗinsa zai tuntubi wasu jam’iyyun siyasa domin su haɗa kai wajen neman kafa abin da ya kira babbar Osun mai ci gaba.

Ya ce:

“Na yi farin ciki da wannan ci gaban, kuma za mu kuma tuntubi wasu jam’iyyu domin mu haɗa hannu wajen gina Jihar Osun mafi girma.”
Dan takarar APGA ya janye daga zaben Osun ya goyi bayan dan takarar APC
Taswirar jihar Osun inda dan takarar APGA ya janye wa dan takarar APC. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Janyewar APGA ba za ta sauya kuri’a ba

Janyewar Adeyemi-Doro a wannan lokaci na kusa da zaɓe ba zai yiwu ya sauya sunayen ’yan takarar da za su kasance a takardar zaɓe a ranar zaɓen ba.

An rufe wa’adin janye sunan ɗan takara daga zaɓen, kuma ana sa ran Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta riga ta fara ko ta kammala shirye-shiryen buga takardun zaɓe da sunayen ’yan takarar da aka tantance.

Sai dai matakin Adeyemi-Doro ya zo ne a wani muhimmin lokaci, yayin da jam’iyyun siyasa ke shiga matakin ƙarshe na yaƙin neman zaɓe.

INEC ta amince da ’yan takara 14 domin fafatawa a zaɓen gwamnan Osun, ciki har da gwamna mai ci, Ademola Adeleke, wanda ke neman ci gaba da mulkinsa.

Kara karanta wannan

Babban Sarki ya kama layi, ya ce ya kamata a hana kowa kamfe a jihar ban da Tinubu

Janyewar ɗan takarar APGA da goyon bayan da ya bai wa APC na ƙara nuna yadda ake samun sauye-sauyen siyasa da haɗa kai tsakanin jam’iyyu yayin da ranar zaɓen 15 ga Agusta ke ƙara kusantowa.

Zaben gwamna: An kashe mutum 18 a Osun

A wani labari, mun ruwaito cewa, an shiga fargabar sake barkewar rikici a Osun yayin da ake ƙara kusantar zaɓen gwamna na 15 ga Agusta.

Jam'iyyar APC ta ce an kashe aƙalla mambobinta 10 tun bayan fara kamfen, yayin da Accord Party ta ce ta rasa mambobi takwas.

Kungiyoyin kare dimokuraɗiyya sun ce an samu hare-haren siyasa 44 da suka yi sanadin mutuwar mutane 13 a jihar tsakanin Oktoba 2025 da Yuni 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com