2027: Shugaba Tinubu Ya Karbi Fom Din Neman Sake Tsayawa Takara a Inuwar APC

2027: Shugaba Tinubu Ya Karbi Fom Din Neman Sake Tsayawa Takara a Inuwar APC

  • Ta tabbata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake tsayawa takara domin neman wa'adi na biyu a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Mai girma Bola Tinubu ya saya fom din na gani ina so da na tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC
  • Sayen fom dai na zuwa ne yayin da lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta kayyade ga jam'iyyu domin fitar da 'yan takara ke kara matsowa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tsaya takara a karkashin inuwar jam'iyyar APC a babban zaben 2027.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ikeja, James Faleke, ya karɓi fom ɗin gani ina so da na tsayawa takara na jam’iyyar APC a madadin Shugaba Bola Tinubu gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu wanda za su fafata wajen neman tikitin APC a zaben 2027

Tinubu ya saya fom din takara
Shugaba Bola Tinubu da James Faleke a wurin saya masa fom din takara Hoto: @imranmuhdz
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa dan majalisar ya karbi fom din ne a ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026.

An karbi fom a madadin Tinubu

Sakataren tsare-tsare na jam’iyyar APC na ƙasa, Suleiman Argungu, ya bayyana buɗe tsarin sayen fom ɗin tare da miƙa su ga Faleke, wanda kuma shi ne wanda ya kafa ƙungiyar goyon bayan Tinubu, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da hakan.

Karɓar fom ɗin da James Faleke ya yi da kuma biyan kuɗinsu da ya kai Naira miliyan 100 a madadin shugaban ƙasar, ya nuna alamar fara fafutukar neman sake zaɓen Tinubu a hukumance.

INEC ta sanya ranakun zaben 2027

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ta ƙasa a ranar Asabar, 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokoki na jihohi zai gudana a ranar Asabar, 6 ga Fabrairu, 2027.

Kara karanta wannan

Bayan na Pantami, an tara wa dan majalisar tarayya miliyoyi domin takara

INEC ta kuma sanar da cewa za a gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam’iyyu, gami da sasanta takaddamar da suka shafi hakan, daga ranar 23 ga Afrilu, 2026, zuwa 30 ga Mayu, 2026.

Haka kuma, INEC ta bayyana cewa za a fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ta ƙasa a ranar 19 ga Agusta, 2026, yayin da na zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi zai fara ranar 9 ga Satumba, 2026.

Shugaba Tinubu zai yi takara a 2027
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wajen taro a fadar Aso Rock Villa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Stanley Osifo zai yi takara da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu wanda za su fafata domin neman tikitin jam'iyyar APC a babban zaben shekarar 2027.

Stanley Osifo ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar neman tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 da ake tunkara.

Hakazalika, Stanley Osifo ya sanar da shirinsa na sayen fom ɗin tsayawa takara na jam’iyyar APC kan kuɗi Naira miliyan 100 gabanin gudanar da zaɓen fitar da gwanin da za a yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng