'Yan Ta'adda Sun Yi Aika Aika a Adamawa, Gwamna Fintiri Ya Sha Alwashi

'Yan Ta'adda Sun Yi Aika Aika a Adamawa, Gwamna Fintiri Ya Sha Alwashi

  • 'Yan ta'adda dauke da makamai sun kai harin ta'addanci wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a jihar Adamawa
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun kai harin ne a karamar hukumar Gombi inda suka hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ziyarci inda ya lamarin ya auku domin ganewa idonsa barnar da aka yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - Aƙalla mutane 29 ne aka kashe biyo bayan wani hari da wasu 'yan ta'adda ɗauke da makamai a jihar Adamawa.

'Yan ta'addan sun kai hare-haren ne a kauyukan Guyaku da Telabala da ke ƙaramar hukumar Gombi ta jihar Adamawa.

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Adamawa
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce maharan sun afka wa yankin ne lokacin da ake gudanar da wasan ƙwallon ƙafa a makarantar firamare ta garin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma ranar Lahadi, 26 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Najeriya suka ki karbar cin hancin N100m

'Yan ta'adda sun yi ta'asa a Adamawa

'Yan ta'addan sun buɗe wuta ba kakkautawa, lamarin da ya tursasa wa mazauna garin gudu zuwa wurare masu aminci cikin ruɗani da fargaba.

Wannan hari yana zuwa ne mako guda bayan wani makamancinsa da ya faru a Mayo Ladde da ke ƙaramar hukumar Hong ta jihar. Maharan sun kuma ƙonata gine-ginen addini.

Wasu mazauna garin sun kasa danne kukan su yayin da suke zaman makokin rashin mambobin iyalansu.

Wani mazaunin Guyaku, Musa Guyaku, ya ce:

“Jiya da yamma, matasa sun shirya wasan ƙwallon ƙafa tsakanin al’ummomi biyu, Zangula da wani ƙauye."
"Ba zato ba tsammani, wasu masu ɗauke da makamai suka far wa garinmu suna harbi ba kakkautawa, inda suka kashe mutane biyu da ke zaune a cikin wata bukka sannan suka ƙona bukkas.”

Lokacin da aka tambaye shi game da jimillar adadin waɗanda suka mutu, ya ce ba zai iya ba da takamaiman adadi ba.

Gwamna Fintiri ya kai ziyara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka malamin addini da iyalansa a Plateau

Gwamna Umaru Fintiri, wanda ya dakatar da sauran harkokin gwamnati, ya ziyarci yankin domin duba halin da ake ciki, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton.

Ya bayyana harin a matsayin abin ban tausayi, inda ya lura cewa ya faru ne jim kaɗan bayan wani makamancinsa a ƙaramar hukumar Hong.

A cewar gwamnan, ya ziyarci yankin ne don ganin barnar da harin ya haifar, wanda ya siffanta da cewa aikin miyagun mambobin Boko Haram ne, da kuma kwantar wa waɗanda abin ya shafa hankali.

'Yan ta'adda sun kashe mutane a Adamawa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa Hoto: @GovernorAUF
Source: Twitter

Gwamna Fintiri ya ba da tabbaci

Ya ba mazauna garin tabbacin cewa gwamnati da hukumomin tsaro suna gudanar da ayyukansu kuma za su tabbatar da kare lafiyarsu. Ya kuma jajantawa basaraken yankin kan wannan rashin da aka yi.

Gwamna Fintiri, wanda ya nuna damuwa ƙwarai, ya jajantawa jama’a tare da tabbatar da cewa kusan mutane 29 ne suka mutu a harin, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki da takaici.

“Za mu ci gaba da yin iyakar ƙoƙarinmu domin su mutanenmu ne, kuma za mu tsaya musu tare da tabbatar da cewa gwamnati ta haɗa kai da sojoji da sauran hukumomin tsaro don ganin an ba su kariya ta gari."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan bayin Allah a Katsina, an samu asarar rayuka

- Ahmadu Umaru Fintiri

'Yan bindiga sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutane 11, yayin wani hari a jihar Katsina.

Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen ne a wani hari da suka kai a kauyen Gurbi da ke karamar hukumar Kankara ta jihar.

'Yan bindigan sun budewa mutanen wuta ne lokacin da suke kokarin tserewa sakamakon harin da suka kawo a kauyen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng