Yadda 'Yan Sandan Najeriya Suka Ki Karbar Cin Hancin N100m
- Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun samu nasarar cafke wasu bata-gari da ke fasakwaurin kayayyakin layin dogo
- An cafke mutanen ne lokacin da suke kan hanyar kai kayayyakin da suka sato zuwa jihar Kwara a yankin Arewa ta Tsakiya
- A yayin bincike, an yi wa jami'an 'yan sanda tayin cin hancin N100m domin su saki kayan tare da mutanen da suka cafke
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jami'an rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) na sashen binciken sirri na musamman (FID-STS), sun ki karbar cin hancin Naira miliyan 100.
Jami'an 'yan sandan sun ki karbar cin hancin ne da wata ƙungiyar masu fasa ƙaurin kayan gwamnati suka yi ƙoƙarin ba su.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sanda, DCP Anthony Placid, ya sanya a shafin X a ranar Litinin, 27 ga watan Afirilun 2026.
'Yan sanda sun cafke masu aikata laifi
Rundunar 'yan sandan ta samu gagarumar nasara wajen kama mutane biyu da ake zargi da yin barna mai yawa ga muhimman ababen more rayuwa na ƙasa tare da ƙwato kayan layin dogo da darajarsu ta haura N400,000,000.
Waɗanda ake zargin, Chisom Goodnews (ɗan shekara 32) da Ahmed Adamu (ɗan shekara 22), an kama su ne a ranar 9 ga Afrilu, 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a garin Akwanga da ke jihar Nasarawa, biyo bayan bayanan sirri masu tushe.
DCP Anthony Okon Placid ya ce samamen ya kai ga kama wata babbar mota (tirela) maƙare da kusan tan 60 na kayayyakin layin dogo da aka sato.
Ya bayyana cewa an ɓoye kayayyakin ne a ƙarƙashin buhunan bawon gyaɗa da nufin kauce wa jami’an tsaro yayin da ake jigilar su daga jihar Bauchi zuwa birnin Ilorin na jihar Kwara.
'Yan sanda sun ki karbar cin hanci
“Binciken farko ya nuna cewa an yi yarjejeniyar biyan direban motar N2.5m domin jigilar kayan da aka sato, yayin da ƙarin bincike ya nuna cewa akwai wani tsari na masu sato kayan da masu karɓa waɗanda ke da alaƙa da juna."
“Yayin gudanar da bincike, jami’an da suka gudanar da samamen sun yi watsi da tayin N100m da aka yi musu da nufin lalata binciken da kuma sakin waɗanda ake zargi tare da kayan da aka kama."
- DCP Anthony Placid
Ya ƙara da cewa an ƙwato babbar motar da aka yi amfani da ita wajen jigilar kayan, kuma ana ci gaba da bincike don kamo sauran mambobin ƙungiyar, ciki har da masu karɓar kayan, da kuma gano wasu ƙarin kayayyakin.

Source: Twitter
An yaba wa jami'an 'yan sanda
“Sufeto Janar na ’yan sanda, IGP Olatunji Rilwan Disu, psc(+), NPM, ya yaba wa jami’an saboda jajircewarsu, tarbiyya, da kuma ƙin karɓar cin hanci, inda ya lura cewa irin waɗannan ayyuka su ne ainihin dabi’un rundunar."
“Rundunar ’Yan Sandan Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen kare kadarorin ƙasa daga masu fasa ƙauri."
- DCP Anthony Placid
Sun cancanci yabo
Sahabi Abdulrahman ya yabawa kokarin da 'yan sandan suka yi wajen kawar da kai daga karbar cin hanci.
"Wannan abin a yaba ne sosai domin cin hanci ba karamar illa yake yi ba ga kasa. Idan jami'anmu za su rika kin karbarsa ba karamin sauyi za a samu ba."
"Cin hanci yana da illa sosai wajen ruguza kasa. Muna yaba masu sosai kan namijin kokarin da suka yi. Allah ya sa saura ma su yi koyi da su."
- Sahabi Abdulrahman
'Yan sanda sun cafke masu leken asiri
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an 'yan sanda a Sokoto sun cafke wasu da ake zargin suna bayar da bayanai ‘yan bindiga bayanai.
Hayatu Hassan Shaffa wanda shi ne kwamishinan 'yan sanda na Sokoto ya ce jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane sun kama wani Aminu Mai Roba daga kauyen Maikulki da ke karamar hukumar Binji.
Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ya karbi shanun ne daga kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa a kauyen Wariya da ke Tangaza.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


