2027: Peter Obi da Wasu Jiga Jigai Sun Gana da Jonathan, an Ji Abin da Suka Tattauna

2027: Peter Obi da Wasu Jiga Jigai Sun Gana da Jonathan, an Ji Abin da Suka Tattauna

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi manyan baki a gidansa da ke Abuja a ranar Litinin, 27 ga watan Afirilun 2026
  • Goodluck Jonathan ya karbi bakuncin tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi da tawagarsa inda suka yi wata ganawa a kebance
  • Peter Obi ya bayyana makasudin ziyarar da suka kai ga tsohon shugaban kasar wanda ya bar mulki a shekarar 2015

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LPa zaɓen 2023, Peter Obi, da wasu shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun gana da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.

Peter Obi da tawagarsa sun gana da tsohon shugaban kasar ne gabanin babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Jonathan ya gana da Peter Obi
Peter Obi na gaisawa da Goodluck Jonathan da sauran tawagarsa Hoto: Peter-The Rock-Obi Movement
Source: Twitter

Peter Obi ya gana da Jonathan

Jaridar Daily Trust ta ce ganawar, wadda aka yi ta a asirce, ta gudana ne a gidan Jonathan da ke Abuja a yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Yusuf Tuggar, ministan Tinubu da ya yi murabus ya ayyana shiga takarar gwamna

Shugabannin Kudu maso Gabas da suka halarci taron sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Enugu, Dr. Okwesilieze Nwodo; tsohon gwamnan Jihar Imo, Achike Udenwa; tsohon shugaban hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC), Chief Onyema Ugochukwu; Sanata Victor Umeh, da dai sauransu.

Dama dai Obi ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC.

Me Peter Obi suka tattauna da Jonathan?

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Obi wanda ya yi magana a madadin shugabannin na Kudu maso Gabas, ya ce sun tuntubi tsohon shugaban ƙasar ne game da babban zaɓen 2027.

Obi ya ce Shugaba Jonathan ya yi wa Najeriya fatan alheri, kuma burinsa shi ne a gudanar da zaɓe mai inganci, adalci da gaskiya a shekarar 2027, sannan ya ƙara da cewa ba za a iya mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya tilo ba.

“Ya yi fatan mu samu zaɓe mai inganci, adalci da sahihanci. Wannan shi ne burinsa. Ba za a iya samun tsarin jam’iyya ɗaya ba. Ba zai iya tallafa wa irin wannan abun ba."
"Babu wanda zai iya iƙirarin cewa shi babban ɗan dimokuraɗiyya ne a ƙasar nan idan aka kalli waɗanda suka jagoranci ƙasar nan ba tare da an sanya shi (Jonathan) a matsayin lamba ɗaya ba."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya zubar da hawaye a taron nuna goyon baya ga Tinubu, an ji dalili

- Peter Obi

Peter Obi ya gana da Jonathan
Goodluck Jonathan na tattaunawa da Peter Obi da tawagarsa yayin ziyarar da suka kai masa Hoto: Peter-The Rock - Obi Movement
Source: Facebook

Shin Jonathan ya goyi bayan takarar Obi?

Jaridar The Punch ta ce da yake magana kan batun amincewa da takararsa ya ce:

“Ba muna maganar amincewa ba ne tukunna. Idan na zama ɗan takara, zan dawo don neman amincewarsa. Yana yi wa ƙasar fatan alheri. Mun zo nan ne don mu tuntube shi."
“Mu, wasu fitattun shugabanni daga Kudu maso Gabas mun zo tuntubar babban tsohon shugabanmu Goodluck Jonathan. Abin da ya faru ke nan. Game da zaɓen 2027 ne kuma komai ya shafi Najeriya ne."
“Yanzu muna kallonsa (Jonathan) a matsayin rukunin da muke kallon tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, tsohon Shugaba Ibrahim Babangida da sauran su, don haka shi ne rukunin da muke kallonsa a yanzu."

An yi wa Peter Obi da Kwankwaso tayin tikiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NDC mai adawa ta mika kokon bararta ga Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso da sauran 'yan adawa sun cimma matsayar da za ta girgiza Tinubu a 2027

Jam’iyyar NDC ta roƙi Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da manyan jiga-jigan ADC da su koma cikinta domin fafatawa zaɓen 2027 mai zuwa.

Ta nuna cewa akwai wa’adin makonni biyu kacal ga Obi da Kwankwaso su shiga cikinta domin samun tikitin shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng