Siyasa Ta Yi Zafi, an Bindige Yaro Ɗan Shekara 12 yayin Kamfen APC
- An samu tashin hankali a Ilesa da ke jihar Osun, bayan an harbi wani yaro mai suna Tobi Ilesanmi, yayin gangamin APC
- Shaidu sun ce harsashi ya same shi ne a cikin shagon mahaifiyarsa, yayin da ake ta harbe-harbe a lokacin jerin gangamin jam’iyyar
- ’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce an kama Kwamishinan Muhalli, Mayowa Adejoorin, domin gudanar da bincike kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilesa, Osun - An samu tashin hankali a wasu sassan Ilesa, Osun, ranar Asabar yayin kamfen zaben gwamnan APC.
Majiyoyi suka ce hakan ya bayan wani rahoto ya ce an harbi wani yaro mai shekaru 12, Tobi Ilesanmi.

Source: Original
Lamarin ya faru ne a garin yayin da jam’iyyar APC ke gudanar da gangaminta, inda aka ce yaron da wasu magoya bayan jam’iyyar sun samu raunuka, cewar Tribune.
Hakan ya haifar da zanga-zanga tare da bukatar a gudanar da bincike cikin gaggawa domin gano ainihin abin da ya haddasa harbe-harben.
Wani ganau ya bayyana cewa yaron yana cikin shagon mahaifiyarsa ne lokacin da harsashin da ya bace daga harbe-harben ya same shi.
Ganau din ya kuma yi zargin cewa an harba bindigogi ne zuwa wajen wasu magoya bayan APC, lamarin da ya jikkata mutane da dama.
Ya ce:
“An kuma jikkata mambobin APC da dama yayin lamarin."
Sai dai, a lokacin da aka wallafa rahoton, ba a fayyace cikakken abin da ya kai ga harbe-harben ba, ko kuma wadanda suka harba bindigogin.
Haka kuma, ba a iya tabbatar da sahihancin mutanen da ake zargi da hannu a harbe-harben ba, saboda bincike kan lamarin yana ci gaba.
Bayan faruwar lamarin, an ce wasu mazauna Ilesa sun gudanar da zanga-zanga, inda suka bukaci hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru.
Sai dai har yanzu ba a iya tabbatar da halin da yaron mai shekaru 12 yake ciki ba, ko kuma ainihin adadin mutanen da suka jikkata.
Lamarin ya faru ne yayin da ake kara zafafa harkokin siyasa a Osun gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
Jam’iyyun siyasa masu hamayya da juna sun kara yawan gangami da yakin neman zabe a sassa daban-daban na jihar yayin da zaben ke kara kusantowa.
Da aka tuntubi rundunar ’yan sandan Osun, kakakinta, DSP Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an kama Kwamishinan Muhalli.
Ya ce an kama Mista Mayowa Adejoorin ne saboda alakarsa da lamarin, bayan jami’an ’yan sanda sun isa wurin da abin ya faru domin fara bincike.
“Nan take aka kai rahoton lamarin, jami’anmu suka tafi wurin, suka katange yankin, sannan suka kwato wasu abubuwa da suka hada da harsasan bindiga.
“Daga cikin abubuwan da aka kwato akwai kwas ɗin harsasan bindiga da aka harba da kuma hulunan jami’an Amotekun."
- Abiodun Ojelabi
Ya kara da cewa an kama Mista Adejoorin a wurin da lamarin ya faru, sannan aka kai shi hedikwatar rundunar domin yi masa tambayoyi.
Kakakin ya ce tambayoyin wani bangare ne na binciken da rundunar ke gudanarwa domin gano cikakken bayani kan abin da ya faru.
Meta Description
Asali: Legit.ng

