OPEC+: UAE Ta Dauki Mataki 1 da Ya Girgiza Saudiyya da Kasuwar Mai Ta Duniya

OPEC+: UAE Ta Dauki Mataki 1 da Ya Girgiza Saudiyya da Kasuwar Mai Ta Duniya

  • Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da ficewarta daga kungiyar kasashen masu arzikin man fetur (OPEC) daga ranar 1 ga watan Mayu
  • Wannan mataki ya girgiza kungiyar OPEC inda ya raunana ikon da take da shi kan sarrafa farashin danyen mai a kasuwan duniya
  • Ficewar kasar na nufin ba za ta sake bin ka'idojin takaita yawan man da take samarwa ba, wanda hakan zai ba ta damar kara yawan man da take hakowa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Dubai – A ranar Talata, 28 ga Afrilun 2026, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta sanar da cewa za ta fice daga kungiyar OPEC da kuma kawancen OPEC+.

Wannan babban sauyi ya zo ne a daidai lokacin da yankin Gabas Ta Tsakiya ke fama da rikicin makamashi sakamakon yakin Iran, wanda ya janyo cikas ga sufurin mai ta mashigin ruwa na Hormuz.

Kara karanta wannan

Tsohon sufeta janar ya zargi APC da neman hana shi takarar gwamna

Hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta fice daga kungiyar OPEC.
Hagu zuwa dama: Ministan makamashin Rasha, Alexander Novak da na Saudiyya, Yarima Abdulaziz bin Salman da na UAE Suhail Al-Mazroui a taron OPEC. Hoto: Haitham EL-TABEI /AFP via Getty Images
Source: Getty Images

UAE ta fice daga kungiyar OPEC

Ministan makamashi na UAE, Suhail Mohamed al-Mazrouei, ya bayyana dalilin wannan mataki a wata tattaunawa ta wayar taraho da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Suhail Mohamed al-Mazrouei ya jaddada cewa ficewar Daular Larabawa daga OPEC ya biyo bayan nazari da yankunan kungiyar bakwai suka yi kan dabarun samar da makamashi na kansu a nan gaba.

Dangane da wannan shawarar, Minista Mazrouei ya bayyana cewa:

"Wannan shawarar siyasa ce, kuma an dauke ta ne bayan mun yi nazari na tsanaki kan manufofinmu na yanzu da na nan gaba dangane da yawan man da muke samarwa."

Tasirin barin UAE daga OPEC ga duniya

Ficewar UAE, wadda ita ce kasa ta hudu mafi karfin samar da mai a cikin kungiyar, zai sa rabon da OPEC+ ke samarwa a kasuwar duniya ya ci gaba da raguwa.

A watan Maris kadai, rabon kungiyar ya fadi zuwa kashi 44% daga kashi 48% da yake a watan Fabrairu, in ji rahoton Dawn.

Kara karanta wannan

Iran ta gana da Rasha, Putin ya yi wa Tehran alkawari kan yaki da Amurka

Masana tattalin arziki na ganin cewa wannan mataki zai ba UAE damar cin gashin kanta wajen kara yawan man da take fitarwa zuwa kasashen waje da zarar an samu saukin barazanar da Iran ke yi wa jiragen ruwa.

Ana ganin cewa kasuwar duniya za ta girgiza yayin da UAE ta fice daga kungiyar OPEC
Hagu zuwa dama: Ministan makamashin UAE, Suhail Mohammed al-Mazroui, da na Saudiyya, Khalid al-Falih (C) da shugaban OPEC Mohammed Barkindo a taron ADIPEC. Hoto" KARIM SAHIB/AFP via Getty Images)
Source: Getty Images

Nasarar siyasa ga Shugaba Donald Trump

Ana kallon ficewar Hadaddiyar Daular Larabawa daga OPEC a matsayin wata babbar nasara ga Shugaban Amurka Donald Trump, cewar rahoton USN.

Shugaba Trump ya dade yana sukar kungiyar OPEC, inda tun a shekarar 2018 ya zarge su da tursasa tsadar farashin mai a duniya.

Trump ya sha bayyana cewa ba zai yiwu Amurka tana bayar da kariya ta soja ga kasashen Gulf ba, sannan kuma su mambobin OPEC su rika amfani da damar suna tsawala wa Amurka farashin mai.

Ana sa ran cewa ficewar UAE zai sa sauran kasashe mambobin OPEC su fara tunanin makomarsu a cikin kungiyar, musamman a wannan lokaci da yakin Iran ke sake sauya fasalin tattalin arzikin duniya.

OPEC ta yi magana kan man Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban gwamnonin OPEC, Ademola Adeyemi-Bero, ya ce Najeriya ta fi karfin gangar danyen mai sama da miliyan daya da take fitarwa.

Kara karanta wannan

'An saka tallafi a man fetur domin rage farashi a Najeriya,' Jami'in matatar Dangote

Ya bayyana cewa kasar na da isassun rijiyoyin mai da yalwar arzikin karkashin kasa da za su ba ta damar samar da fiye da ganga miliyan biyu a kullum.

Mista Adeyemi Bero ya ba da tabbacin hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da daga likkafar kasar nan a fannin fitar da danyen mai a idon duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com