'Yan Bindiha Sun Yi Awon Gaba da Manoma, Sun Bukaci N100m

'Yan Bindiha Sun Yi Awon Gaba da Manoma, Sun Bukaci N100m

  • Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne dauke da makamai sun sace manoma biyu a ƙauyen Parubber da ke jihar Ondo
  • Maharan sun nemi a biya Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa domin su sako waɗanda suka sace
  • Jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da Amotekun sun fara haɗin gwiwar bincike domin ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ondo - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da manoma biyu a ƙauyen Parubber da ke ƙaramar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo ta jihar Ondo.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bukaci a biya su kuɗin fansa har Naira miliyan 100 kafin su sako mutanen da suka sace.

'Yan bindiga sun sace manoma a Ondo
Taswirar jihar Ondo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Vanguard ta ce wata majiya daga cikin iyalan waɗanda abin ya shafa ta ce an yi wa manoman kwanton ɓauna ne a gonakinsu a ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026 kafin maharan su tafi da su cikin wani daji da ke kusa.

Kara karanta wannan

"Mun bar ku da Allah': Mazauna Sokoto sun tura sako ga Gwamna kan rashin tsaro

Fasto ya tsallake rijiya da baya

Ɗaya daga cikin manoman da ya tsira daga harin, Fasto Yemi Omowale, ya ce an kai rahoton lamarin ga rundunar ƴan sanda da kuma Hukumar Tsaron Jihar Ondo (Amotekun).

Omowale, wanda ke kiwon aladu a ƙauyen Parubber da ke kan titin Ondo zuwa Ife, ya bayyana yadda lamarin ya faru.

"Ina da gonar kiwon aladu a ƙauyen Parubber da ke kan titin Ondo zuwa Ife a ƙaramar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo. Mun je gonar da safe domin ba dabbobinmu abinci.
"Tsakanin ƙarfe 12:00 na rana da 1:00 na rana a ranar Litinin, muna aiki a waje ne sai na ga wani mutum sanye da abin rufe fuska ɗauke da bindigar AK-47 yana tafiya wajen ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, Adetan Adebanjo Gbemi, saboda ba mu tsaya tare ba."

Maharan sun nemi Naira miliyan 100

A cewarsa, maharan sun tuntubi matar ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Trump ya rattaba hannu kan dokokin da za su kawo cikas ga 'yan Najeriya da wasu kasashe

"Suna ci gaba da kiran matar wanda aka sace suna tambayarta adadin kuɗin da ta samu. Muna roƙon hukumomin tsaro da gwamnati su taimaka wajen ceto ɗan'uwanmu da 'yar'uwarmu cikin ƙoshin lafiya."

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da lamarin

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Ondo, DSP Jimoh Abayomi, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce hedikwatar rundunar ƴan sanda ta Oke-Igbo ta samu rahoton cewa mutanen sun ɓace.

Abayomi ya bayyana cewa an tura haɗaɗɗiyar tawagar jami'an tsaro, wadda ta haɗa da jami'an rundunar ƴan sanda ciki har da sashen yaƙi da garkuwa da mutane, jami'an Amotekun, mafarauta da masu sintiri na sa-kai domin gudanar da bincike da ceto waɗanda aka sace.

'Yan bindiga sun sace manoma a Ondo
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun nada kwamanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindigan da ke karkashin fitaccen jagora, Ado Aleiro, sun nada sabon kwamandan da zai jagoranci ayyukansu bayan kashe Kachalla Iliya Mai Rasha.

Majiyoyi sun nuna cewa kungiyar na kokarin sake tsara ayyukanta a jihar Zamfara bayan mutuwar Mai Rasha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng