Shiriya daga Allah: Yadda Karamin Abu Ya Sa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Ya Daina Shan Giya

Shiriya daga Allah: Yadda Karamin Abu Ya Sa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Ya Daina Shan Giya

  • Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana yadda kalaman wani mutumi a kasar Somaliya suka jawo ya daina shan giya gaba daya
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce duk da kasancewarsa Fasto, yana shan giy amma daga baya ya daina harka da barasa
  • Oainbajo ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa a tsakanin 2015 zuwa 2023 lokacin mulkin Marigayi Muhammadu Buhari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bada labarin yadda wani lamari da bai taka kara ya karya ba, ya sa ya daina shan giya gaba ɗaya.

Farfesa Osinbajo ya ce duk da kasancewarsa malamin coci, yana shan giya musamman wacce ake kira da 'jar giya' lokaci zuwa lokaci.

Yemi Osinbajo.
Farfesa Yemi Osinbajo a wani taron kasashen Afurka da ya wakilci Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A rahoton da jaridar Punch ta tattaro, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce daga baya ya daina shan giya gaba daya.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Peter Obi ya bayyana dalilin ganawa da Jonathan

“Na kan sha jar giyar inabi wani lokaci, haka kuma ina son giya,” in ji shi

Sai dai ya ce wani abu da ya faru a birnin Mogadishu da ke kasar Somaliya, lokacin da yake aiki da Majalisar Dinkin Duniya ya canja masa ra’ayi har ta kai ga ya daina shan giya.

Maganar da ta sa Osinbajo ya daina shan giya

Ya ce wata rana Lahadi bayan ya yi wa’azi a taron ibada, yana hanyarsa ta zuwa siyan kwalaben giya biyu domin komawa daki ya karanta Littafi Mai Tsarki.

Osinbajo ya ce da ya shiga wani gidan cin abinci a cikin unguwar da gidajen ma'aikatan Majalisar dinkin duniya suke, ya tarar da abokan aikinsa daga kasashe daban-daban suna shan giya.

A cewarsa, da suka gan shi, sai suka ɓoye giyarsu, yayin da ya tambayi wani abokinsa dan ƙasar Denmark dalilin da ya sa ya ɓoye giya, sai ya ce masa:

“Kai fasto ne, ba za mu iya shan giya a gabanka ba."

Darasin da Farfesa Osinbajo ya dauka

Kara karanta wannan

Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48

Farfesa Osinbajo ya ce wannan lamari ya zama masa kamar saƙo daga Allah, wanda ya sa ya fahimci ma’anar cewa komai na iya halatta ga bil'adama amma ba duka suke da amfani ba.

Ya ce tun daga wannan rana da mutumin ya gaya masa wannan magana, bai ƙara shan giya ba, cewar rahoton Vanguard.

Osinbajo.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Source: Twitter

Yemi Osinbajo ya ba da wannan labari ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Bidiyon ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu suka ga labarin a matsayin abin dariya kuma mai ma’ana, yayin da wasu suka yi amfani da damar wajen tattauna rayuwarsa da rawar da ya taka a siyasa.

Osinbajo ya nemi matasa su shiga siyasa

A wani labarin, kun ji cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya buƙaci ƴan Najeriya, da su rika shiga harkokin siyasa domin amfani da ita a matsayin hanyar samar da shugabanci nagari.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna cewa duk da mummunan suna da siyasa ke da ita a halin yanzu, ita ce kaɗai hanyar gyara kasa ta kafa jagoranci nagari.

Yayin da yake magana kan matasan Najeriya da ke da burin shiga ofisoshin gwamnati, ya nuna cewa wajibi ne su kasance cikin shiri ta fuskar ilimi tare da fahimtar yadda shugabanci ke aiki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262