Manyan Labarai A Yau
Wasu mutane da ake zargin 'yan daban siyasa ne sun hallaka wani malamin Islamiyya a jihar Bauchi. Sun kashe mutumin ne bayan takaddama ta barke tsakaninsu.
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi ta'aziyyar rasuwar 'ya'yan tsohon mataimakin gwamnan Bauchi.
Dan majalisar wakilai daga jihar Plateau, Yusuf Gagdi, ya nuna adawarsa da shirin gyara halin 'yan ta'adda. Ya bayyana cewa ba su cancanci ci gaba da rayuwa ba.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus daga kujerarsa kan matsalar rashin tsaro.
Ozonna Soludo, dan gwamnan jihar Anambra ya jawo takaddama a kafafen sada zumunta bayan ya saki bidiyon wakar sukar manyan mutane har da mahaifinsa.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi magana kan sulhu da 'yan bindiga. Gwamnan ya bayyana cewa ba zai tattauna ko sulhu da 'yan bindiga ba.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyukan jihar Sokoto. Hare-haren sun jawo mutane da dama sun tsere daga gidajensu don samun tsira.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa. Ya kafa hujja kan sabon bayanin asusun IMF.
Rundunar 'yan sandan jihar Imo, ta fito ta yi magana kan batun cewa wasu da ake zargin makiyaya ne, sun kona dakin kwaanan dalibai kurmus a Owerri.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari