Tinubu Ya Sake Neman Bukata wajen Majalisa bayan Amincewa Ya Runtumo Bashi

Tinubu Ya Sake Neman Bukata wajen Majalisa bayan Amincewa Ya Runtumo Bashi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasika ga majalisar dattawa domin neman amincewarta kan nade-naden da ya yi
  • Mai girma Bola Tinubu ya nemi majalisar da ta amince da nade-naden da ya yi a majalisar gudanawar hukumar NHRC
  • Shugaban kasar ya gabatar da sunayen mutane 15 wadanda ya zabo daga fannoni daban-daban domin su yi aiki a hukumar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Abuja, Najeriya - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sabuwar wasika ga majalisar dattawa.

Shugaba Tinubu ya wasiƙar ne yana neman tantancewa da kuma tabbatar da mutane 15 da aka zaɓa domin shiga hukumar kare haƙƙin dan adam ta kasa (NHRC).

Tinubu ya aika wasika ga majalisar dattawa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar a ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

'Me ka tsinana a shekaru 4': Malamin addini ya kalubalanci tazarcen Tinubu

Wace bukata Tinubu ya nema a wajen majalisa

Wasiƙar da shugaban kasar ya aike tana neman sake kafa majalisar gudanarwar ne daidai da tanadin doka, jaridar Thisday ta kawo labarin.

Jerin sunayen ya ƙunshi zaɓaɓɓun mutane daga sassa daban-daban na kwararru, ciki har da fannin yaɗa labarai da na shari’a.

Tinubu ya zabo manyan mutane

A cikin jerin sunayen akwai shugaban kungiyar Editoci ta Najeriya kuma Editan jaridar Vanguard, Mista Eze Anaba; da Dr. Salamatu Hussaina Suleiman, wadda aka gabatar a matsayin shugabar majalisar gudanarwar, yayin da Dr. Anthony Ojukwu (SAN) zai ci gaba da zama shugaba.

Sauran mambobin da aka zaɓa sun haɗa da: Mrs. Roseline Tasha, Adam Yubak Baku, ACG Felix Lawrence, Mr. Edmund Chinonye, Mr. Chinonye Obiaku (SAN), Oluwakemi Asiwaju Okere-Odo, Farfesa Adedeji Ogunji, Kingsley Chidozie, Mohammed Adelodu, Maupe Ogun Yusuf, da kuma Otunba Francis Meshioye.

Haka kuma an zaɓi Patience Patrick da Hawwa Ibrahim a matsayin mambobi a majalisar gudanarwar hukumar.

Kara karanta wannan

Majalisa ta cimma matsaya kan bukatar Tinubu ta runtumo bashin $516.3m

Tinubu ya aika wasika ga majalisar dattawa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Tinubu ya yi nade-nade a hukumar NHRC

Shugaban ƙasar ya ce an yi waɗannan naɗe-naɗe ne bisa ga tanadin sashe na 2(3) na dokar kafa hukumar kare haƙƙin dan Adam ta kasa (2010), wadda ta ba shi ikon kafa hukumar gudanarwa muddin majalisar dattawa ta amince.

Ya bayyana cewa sake kafa majalisar gudanarwar ya zama dole domin haɓaka ƙarfin hukumar da kuma ba ta damar gudanar da aikinta yadda ya kamata wajen haɓakawa da kare haƙƙin ɗan adam a faɗin ƙasar.

Bayan gabatar da wannan buƙata, majalisar dattawa ta tura sunayen zuwa kwamitin shari’a, haƙƙin dan adam da lamuran shari’a na majalisar domin tantancewa tare da gabatar da rahoto nan da mako biyu.

Majalisa ta amince Tinubu ya karbo bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta amince shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya karbo bashin $516.3m daga kasar waje.

Majalisar wakilan ta amince a karbo bashin &516.3m daga bankin Deutsche Bank AG domin samar da kuɗaɗen gina sashe na 1 (bangare na 1A da 1B) na aikin babban titin Sokoto zuwa Badagry.

Amincewar ta biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar kan tallafi, rance da sarrafa bashi yayin zaman majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng