Shugaba Tinubu Ya Tuna da Mutanen da Hare Hare Suka Shafa a Plateau, Ya ba da Tallafin Kudi

Shugaba Tinubu Ya Tuna da Mutanen da Hare Hare Suka Shafa a Plateau, Ya ba da Tallafin Kudi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki na jihar Plateau kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
  • A yayin taron, Shugaban kasar ya bukaci su zakulo hanyoyin da za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali
  • Hakazalika, Tinubu ya amince da ba da tallafin kudi ga mutanen da kashe-kashen da aka yi kwanan nan ya suka shafa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin N2bn ga mutanen da kashe-kashen da aka yi kwanan nan a jihar Plateau ya shafa.

Shugaba Tinubu ya amince da ba da tallafin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalolin da yawaitar rikice-rikicen da ake yawan samu a yankin ya haifar.

Tinubu ya ba da tallafi ga mutanen Plateau
Shugaba Bola Tinubu tare da wasu masu ruwa da tsaki daga Plateau Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce an sanar da wannan amincewa ne ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya gwangwaje sababbin jakadun Najeriya da babbar kyauta

Su waye za su amfana da tallafin?

An bayyana hakan ne yayin wata gagarumar ganawa tsakanin shugaban kasar da wasu wakilan masu ruwa da tsaki na jihar Plateau mutum 32, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang.

Ministan jin kai da yaƙi da talauci, Mohammed Dorro, ya bayyana cewa an ware waɗannan kuɗaɗe ne musamman ga waɗanda harin ranar 29 ga Maris ya shafa a Angwan Rukuba, da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Bola Tinubu ya yi kira ga shugabannin Plateau

A wurin taron, wanda aka kwashe kusan sa’o’i uku ana yi, Shugaba Tinubu ya buƙaci masu ruwa da tsakin da su koma gida tare da sabon ƙuduri na wanzar da zaman lafiya, haƙuri, da sulhu, inda ya jaddada buƙatar kawo ƙarshen yawaitar tashin hankalin da ya addabi jihar.

A cewarsa, haƙuri da mutunta juna su ne ya kamata su zama harsashin kowane irin ƙudurin sasanci.

Shugaban ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta kamo tare da tona asirin duk wasu wakilan tada zaune-tsaye, inda ya ba da tabbacin cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani na doka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake neman bukata wajen majalisa bayan amincewa ya runtumo bashi

Ya jaddada cewa adalci, nuna gaskiya, da rashin nuna bambanci su ne mabuɗan dawo da kwanciyar hankali.

Shugaba Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki a Plateau
Shugaba Bola Tinubu yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a Plateau Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwamnan jihar Plateau ya yi jawabi

Gwamna Mutfwang, a nasa jawabin, ya godewa Shugaban ƙasa bisa sa baki da kuma shugabancin da ya nuna, inda ya lura cewa taron ya nuna wani yanayi na haɗin kai da ba a saba gani ba a tsakanin shugabannin siyasar Plateau.

“Wannan shi ne karon farko da dukkan tsofaffin gwamnonin jihar suka taru a ɗaki ɗaya don wannan dalili."
"Hakan yana nuna sabon yanayi a Plateau, mun ƙuduri aniyar kawar da rarrabuwar kawuna domin gina jihar da dukanmu za mu yi alfahari da ita.”

- Gwamna Caleb Mutfwang

Bola Tinubu ya yi kyauta ga jakadu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje sababbin jakadun Najeriya da kyaututtuka.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ba da kyautar filaye a babban birnin tarayya Abuja ga sababbin jakadun wadanda za su wakilci Najeriya a kasashen waje.

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce Shugaba Tinubu ya amince da hakan ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng