Shugaba Tinubu Ya Gwangwaje Sababbin Jakadun Najeriya da Babbar Kyauta

Shugaba Tinubu Ya Gwangwaje Sababbin Jakadun Najeriya da Babbar Kyauta

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da kyauta ga sababbin jakadun da aka nada wadanda za su wakilci Najeriya a kasashen waje
  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince a ba su filaye
  • ​Nyesom Wike ya bayyana cewa Tinubu ya amince a ba su filayen ne domin su mallaki wuraren zama a babban birnin tarayya Abuja

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Bola Tinubu ya amince a warewa sababbin jakadun da aka naɗa filaye a Abuja.

Wike ya ce Shugaba Tinubu ya amince da hakan ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da ƙarfafa dangantaka ta kusa da Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya ba jakadu filaye
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tashar Channels ta ce ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ban girma da jakadun, ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar harkokin waje, Dunoma Umar Ahmed, suka kai masa a gidansa da ke Abuja, ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake neman bukata wajen majalisa bayan amincewa ya runtumo bashi

Meyasa Bola Tinubu ya ba jakadu filaye?

Yayin da yake jawabi, Ministan ya ce shawarar shugaban ƙasar ta samo asali ne daga muradin ganin cewa wakilan Najeriya suna da muhallin kansu na dindindin a Abuja lokacin da suka dawo don bayar da rahoton ayyukansu lokaci-lokaci.

“Shugaban kasa ya yi amanna cewa yawancinku ba ku da gida a Abuja… zai ƙarfafa ku don ku ga yadda za ku gina wurin da za ku zauna. Kafin ku tafi a safiyar nan, kowane ɗayanku ya kamata ya mallaki fom ɗin neman fili a Abuja."

- Nyesom Wike

Haka kuma ya bayyana cewa wannan karimci an yi shi ne da nufin zurfafa kasancewar jami’an diplomasiyya a babban birnin Najeriya tare da haɓaka hulɗa tsakanin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje da hukumar FCTA, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Nyesom Wike ya ba jakadu shawara

Wike ya bukaci jakadun da su kare martabar Najeriya a duk inda suka samu kansu.

Kara karanta wannan

Yadda minista ya yi murabus duk da Shugaba Tinubu bai so hakan ba

“A taƙaice, ku ne madubin wannan ƙasa. Yadda duniya take kallonku, haka za ta kalli Najeriya."

- Nyesom Wike

Wike ya ba sababbin jakadu shawara
Nyesom Wike tare da wasu daga cikin sababbin jakadun da aka nada Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

Ya umarce su da su isar da kyakkyawar manufa da abubuwan da Shugaba Tinubu ya sa a gaba yadda ya kamata, musamman wajen jawo masu zuba hannu jari daga ƙasashen waje da ƙarfafa haɗaka da ƙasashen duniya.

“Shugaban ƙasa ya yi tafiye-tafiye da dama don jawo masu zuba hannun jari daga ƙasashen waje da haɗaka. Yanzu ne aikinku na ƙarfafa wannan ƙoƙari ta hanyar gina kwarin gwiwa kan Najeriya a matsayin wurin da ya dace a zuba jari."

- Nyesom Wike

Tinubu ya nemi bukata wajen majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasika zuwa ga majalisar dattawan Najeriya.

Shugaba Tinubu ya aika wasiƙar ne yana neman tantancewa da kuma tabbatar da mutane 15 da aka zaɓa domin shiga hukumar kare haƙƙin dan adam ta kasa (NHRC).

Jerin sunayen ya ƙunshi zaɓaɓɓun mutane daga sassa daban-daban na kwararru, ciki har da fannin yaɗa labarai da na shari’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng