Daga Sama har Ƙasa: Gwamna Ya Mallakarwa Tinubu Ƙuri'un Jiharsa a 2027
- Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya ce APC za ta samu gagarumar nasara a zaɓen 2027, tare da tabbatar wa Tinubu cikakken goyon baya
- Kefas ya ce Taraba za ta tattara kuri’u masu yawa ga Shugaba Bola Tinubu, saboda ayyukan gwamnatin tarayya da ta ce suna tallafa wa jihar
- Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar ba ta neman kuri’u kaɗai ba, tana kuma ƙoƙarin inganta rayuwar ’yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - Gwamnan Taraba, Dakta Agbu Kefas, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na shirin samun gagarumar nasara a jihar.
Gwamna Kefas ya kuma yi alƙawarin cewa Taraba za ta samar da kuri’u ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC “daga sama har ƙasa”.

Source: Facebook
Gwamna Kefas ya bayyana hakan ne a Jalingo yayin da yake karɓar baƙuncin Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, cewar Leadership.
Jam'iyyar da yan Taraba suka fi so
Yilwatda ya je Taraba ne domin halartar wasu shirye-shiryen bikin cikar sa shekaru 58, ciki har da wani shirin tallafin lafiya ga mazauna jihar.
Kefas ya ce APC ta zama jam’iyyar da al’ummar Taraba suka fi so, saboda gwamnatocin jam’iyyar a matakin tarayya da jiha suna mai da hankali kan bukatun jama’a.
Ya ƙara da cewa jihar za ta tara kuri’u daga makwabtanta domin tabbatar da Shugaba Tinubu ya samu dukkan kuri’un da yake bukata.
Ya ce:
“Taraba jiharka ce. Taraba ta APC ce. Abin da Mista Shugaban Ƙasa ya yi, da irin sha’awar da ya nuna wa Taraba, ba za a iya auna shi da kuri’ar da za mu ba shi ba.
“A Taraba, ba mu fafata zaɓe da wata jam’iyya ko wani mutum. Mu kawai muna da ’yan takarar wasu jam’iyyun da ke shiga zaɓe tare da mu.”

Source: Original
Alkawarin da gwamnan Taraba ya yi ga Tinubu
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta tattara goyon bayan Shugaba Tinubu, saboda gwamnatin tarayya ta nuna himma wajen bunƙasa Taraba da tabbatar da tsaron jihar.
Ya yi nuni da amincewar kwanan nan da Shugaba Tinubu ya bayar na kafa rundunar sojojin Najeriya mai hedikwata a Jalingo, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron ƙasa da haɗin kan Najeriya.
Kefas ya tabbatar wa APC cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin taimaka wa gwamnatin Tinubu wajen cimma manufofinta na ci gaba.
Kefas ya ce:
“Kwanan nan, Shugaban Ƙasa ya amince da kafa rundunar sojojin Najeriya da hedikwatarta za ta kasance a Jalingo, Taraba.
Waɗannan manyan abubuwa ne da Mista Shugaban Ƙasa ya yi domin tabbatar da haɗin kai da ci gaban ƙasar nan."
Gwamnan ya kuma bayyana fatansa na ganin Taraba ta zama ɗaya daga cikin manyan wuraren yawon buɗe ido a Najeriya, yana mai cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin bunƙasa damar yawon buɗe ido da jihar ke da ita.
Benue ta shirya ba Tinubu kuri'u miliyan daya
Kun ji cewa mataimakin Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ode, ya ce jihar na da shirin samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri'u miliyan 1 a zaben 2027.
Ya ce gwamnatin Gwamna Hyacinth Alia za ta tattara mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar da al'ummar Benue domin tabbatar da cika wannan alƙawari.
Ode ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar tawagar Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Bayo Onanuga.
Asali: Legit.ng


