Tashin Hankali: Sojoji 42 Sun Mutu a Hanyar Dawowa daga Karbar Horo a Nijar
- Akalla jami’an rundunar sojin Jamhuriyar Nijar 42 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da motocin bas biyu
- Hatsarin ya faru ne kusa da Doukou Doukou, kimanin kilomita 55 daga Madaoua, yayin da sojojin ke tafiya bayan kammala horonsu
- Wasu jami’an soji 18 na kwance cikin mawuyacin hali bayan hatsarin, yayin da ake ci gaba da bincike kan musabbabin faruwar lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Nijar - Akalla jami’an rundunar sojin Jamhuriyar Nijar 42 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da motocin bas biyu kusa da Doukou Doukou, kimanin kilomita 55 daga Madaoua.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun ce hatsarin ya faru ne a ranar Juma’a, 7 ga watan Agustan 2026.

Source: Getty Images
Sojojin Nijar sun yi hatsarin mota
Labarin ya fito ne daga Zagazola Makama, wata kafar da ke bibiyar harkokin yaƙi da ta’addanci, wadda ta nakalto majiyoyin tsaro na cewa wadanda suka mutu mataimakan jami’an soji ne da ba sa rike da manyan mukamai.
An ce jami’an sun kammala horonsu ne a ranar Alhamis, kafin su shiga motocin bas din domin tafiya, inda hatsarin ya afku.
Majiyoyin tsaron sun ce wasu jami’an soji 18 da suka tsira daga hatsarin suna cikin mawuyacin hali, inda aka ce wasu daga cikinsu suna cikin suma.
Har zuwa lokacin hada rahoton, ba a bayyana cikakken bayani kan yadda hatsarin ya faru ba.
Zagazola Makama ta ce lamarin ya sake haifar da tambayoyi kan tsarin sufuri da ake amfani da shi wajen jigilar jami’an soji.
An yi tambaya kan motocin sufuri
A cewar rahoton, akwai zargin cewa motocin bas din da ke jigilar sojojin kamfanin sufuri ne mai zaman kansa ke sarrafa su, duk da cewa rundunar sojin na da nata motocin jigilar dakaru.
Sai dai ba a iya tabbatar da zargin cin hanci da rashawa da ake dangantawa da amfani da motocin kamfanin masu zaman kansu ba.
Rahoton ya ce hatsarin na iya haifar da sabon bincike kan harkokin kayan aiki da dabarun jigilar dakaru da kuma matakan tabbatar da lafiyarsu, musamman jami’an da suka kammala horo kwanan nan.

Source: Getty Images
Ba a tabbatar da adadin ba
Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa ba a iya tabbatar da kanta kan adadin mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata ba.
Haka kuma, ba a iya tabbatar da zargin da ake yi kan dalilin da ya sa aka yi amfani da motocin wani kamfani mai zaman kansa wajen jigilar sojojin ba.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara mayar da hankali kan inganta tsarin sufuri da tsaron jami’an soji yayin gudanar da ayyukansu a Jamhuriyar Nijar.
Sojojin Nijar sun kori kamfanin Faransa
A wani labari, mun ruwaito cewa, ma'aikatar makamashi ta Faransa, Orano, ta bayyana cewa gwamnatin sojin Nijar ta karɓi ikon wajen hako ma'adanin uranium na ƙasar.
Wannan ya biyo bayan juyin mulki a watan Yulin bara, inda sojojin suka ce za su sake duba dokokin hakar ma'adanai da kamfanonin waje ke yi.
Legit ta tattauna da wani jami'in DSS a kan jin matakin da suke dauka na samar da tsaro a Najeriya yayin da aka kulla yarjejeniya da Faransa.
Asali: Legit.ng

