Ana tsaka da Rade Radin Tsanantar Rashin Lafiyar Khamenei, Ya Saki Wani Bidiyo
- Wasu kafofin watsa labaran Iran sun wallafa wani tsohon bidiyon Mojtaba Khamenei, wanda ya nuna shi cikin koshin lafiya
- Mojtaba bai bayyana a bainar jama’a ba tun bayan harin Amurka da Isra’ila da ya kashe mahaifinsa, Ali Khamenei, a watan Fabrairu
- Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce sadarwa da Mojtaba tana da wahala a yanzu, yayin da Donald Trump ya yi ikirarin yana cikin mawuyacin hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Wasu kamfanonin yada labarai a Iran ya sake wani sabon bidiyon jagoran addinin Musulunci, Mojtaba Khamenei.
Kafar da ke karkashin kulawar gwamnati, ya wallafa wani bidiyon Mojtaba Khamenei da ba a bayyana ranar daukarsa ba ana cikin rade-radin lafiyarsa.

Source: Getty Images
An saki bidiyon Mojtaba Khamenei
Mojtaba shi ne sabon Jagoran Juyin Juya Halin Iran, kuma ba a gan shi bainar jama’a ba tun bayan harin Amurka da Isra’ila, cewar Times of India.
Harin na ranar 28 ga Fabrairu ya kashe mahaifinsa kuma tsohon Jagoran Juyin Juya Halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda rahotanni suka bayyana
Kamfanin Mehr ya wallafa bidiyon ne a ranar Asabar, inda ya ce bidiyon ya nuna Jagoran Juyin Juya Halin, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, a karon farko
Bidiyon na tsawon dakikoki 12 ne, kuma ya nuna Mojtaba zaune kan tabarma a wani daki, yana mu’amala da wasu mutane da ke zaune kusa da shi
Mojtaba Khamene'i da ke sanye da rawani baki da kuma doguwar riga mai launin toka kan farar tufafi, ya bayyana cikin yanayin da ke nuna koshin lafiya
Rahotanni sun ce Mojtaba ya samu munanan raunuka a fuska da kafa sakamakon harin da aka kai a ranar 28 ga Fabrairun 2026, sai dai ba a bayyana lokacin ko wurin da aka dauki wannan sabon bidiyon ba.
A ranar 20 ga Maris, gidan talabijin din gwamnati na IRIB ya kuma wallafa wani bidiyo makamancin wannan na Mojtaba.
Gidan talabijin din ya ce bidiyon na farko ne da ke nuna Mojtaba yana koyar da ilimin addini, amma bai bayyana ranar ko wurin daukar bidiyon ba.

Source: Getty Images
Ina Mojtaba Khamenei yake?
Tun bayan nada shi a matsayin Jagoran Juyin Juya Halin Iran na uku a ranar 8 ga Maris, Mojtaba ya fitar da wasu rubutattun bayanai ta kafafen gwamnatin Iran
Sai dai dan shekaru 56 bai wallafa hotonsa ko wani faifan muryarsa ba tun bayan nada shi, haka kuma, ba a gan shi a bikin jana’izar mahaifinsa da aka gudanar a watan da ya gabata ba, cewar Sunday Guardian.
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana a wannan makon cewa sadarwa da Mojtaba a halin yanzu tana da matukar wahala.
Ya ce yana da wahalar tuntubar Mojtaba a yanzu, amma kasancewarsa a matsayin Jagoran Juyin Juya Halin na da matukar muhimmanci wajen bai wa Iran karfin guiwa.
Dalilin rashin sake muryar Mojtaba Khamenei
An ji a baya cewa wasu rahotanni sun bayyana dalilin da ya sa har yanzu hukumomi a Iran ba su fitar da muryar jagoran addini, Mojtaba Khamenei ba.
Rahoton ya bayyana cewa masana na iya gano wuri, lokaci da na'urar da aka yi rikodi ta hanyar nazarin amo, wutar lantarki da sautin muhalli.
Haka kuma fasahar tantance murya na iya gano wasu bayanai kan lafiyar mai magana, yanayin numfashinsa, bugun zuciya.
Asali: Legit.ng


