Shugaba Tinubu Ya Yi Sauyi a Gwamnatinsa, Ya Nada Sababbin Ministoci
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin muhimman nade-nade a majalisar ministocinsa sakamakon sauyin da aka samu
- Mai girma Bola Tinubu ya daga darajar karamar Ministar harkokin waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu zuwa mukamin Ministar harkokin waje
- Hakazalika, shugaban kasar ya nada karamin Ministan harkokin waje wanda zai jira tantancewa majalisar domin amincewa da nadin da aka yi masa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja, Najeriya - Shugaban kasar Najeriya, mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya yi sababbin nade-nade a gwamnatinsa.
Shugaba Tinubu ya naɗa Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin Ministar harkokin waje ta Najeriya.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X a ranar Laraba, 29 ga watan Afirilun 2026.
Bola Tinubu ya daga darajar Bianca Ojukwu
Shugaba Tinubu ya yi nadin ne biyo bayan murabus ɗin Ambasada Yusuf Tuggar, wanda ya ajiye aiki domin shiga takara a zaɓen 2027.
Ambasada Odumegwu-Ojukwu ta taɓa riƙe muƙamin karamar Minista a ma’aikatar harkokin waje a baya.
Tinubu ya nada Ministan harkokin waje
Haka zalika, shugaban ƙasar ya nada Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin sabon karamin Ministan harkokin waje, wanda ke jiran tantancewar Majalisar dattawa.
Kafin naɗinsa, Ambasada Enikanolaiye, wanda ɗan jihar Kogi ne, ya yi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin waje da hulɗar kasa da kasa.
Enikanolaiye fitaccen jami’in diflomasiyya ne kuma gogaggun ma’aikacin gwamnati wanda ya kwashe sama da shekaru 30 yana aiki a fannin huldar ƙasashen waje na Najeriya.
Ya taɓa zama babban sakatare a ma’aikatar harkokin waje, kuma ya riƙe muhimman mukaman diplomasiyya a biranen Addis Ababa, Belgrade, Ottawa, London, da New Delhi.

Source: Twitter
Tinubu ya taya ministocin murna
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa waɗannan naɗe-naɗe suna daga cikin ƙoƙarin da ake yi na sake fasalin tsarin manufofin harkokin waje na Najeriya domin samun inganci, kyakkyawar hulɗa, da ƙarfafa haɗaka da ƙasashen duniya.
Shugaba Tinubu ya taya waɗanda aka naɗan murna, sannan ya buƙace su da su yi aiki tuƙuru domin bunƙasa maslahar Najeriya, haɓaka diflomasiyyar tattalin arziƙi, da kuma kare jin daɗin ’yan Najeriya a gida da kuma ƙasashen waje.
Shugaba Tinubu ya ba mutanen Plateau tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada tallafi ga mutanen da hare-haren jihar Plateau suka ritsa da su.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin N2bn ga mutanen da kashe-kashen da aka yi a Angwan Rukuba a jihar Plateau ya shafa.
Mai girma Bola Tinubu ya amince da ba da tallafin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalolin da yawaitar rikice-rikicen da ake yawan samu a yankin ya haifar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

