Sojoji Sun Samu Nasarar Kashe 'Yan Ta'adda a Borno, an Yi Masu Gagarumar Barna

Sojoji Sun Samu Nasarar Kashe 'Yan Ta'adda a Borno, an Yi Masu Gagarumar Barna

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan ta'adda a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Sojojin sun samu nasarar hallaka tsagerun 'yan ta'adda tare da lalata wuraren da suke fakewa domin gudanar da rayuwarsu
  • Hakazalika, dakarun sojojin ba su yi kasa a gwiwa ba wajen kwato tarin bindigogi da alburusai daga hannun 'yan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda 18 yayin artabu a jihar Borno.

Sojojin sun kuma ƙwato dumbin makamai da alburusai a kusa da gadar Azir da ke yankin Timbuktu da kuma dajin Bulabulin a jihar Borno.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Borno
Dakarun sojojin Najeriya a fagen fama Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafin X a ranar Laraba, 29 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan an yi masa tayin takara, shugabannin NDC sun gana da Kwankwaso a gidansa

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

Laftanar Kanal Sani Uba ya ce sojojin sun kashe 11 daga cikin ’yan ta’addan ne a dajin Bulabulin yayin da aka kashe bakwai a yankin Timbuktu.

Ya bayyana cewa dakarun 'Sector 2' ne suka gudanar da waɗannan ayyukan guda biyu cikin haɗin gwiwa da sashen sojojin sama na rundunar OPHK.

"A yankin dajin Bulabulin, dakarun 'Sector 2' na OPHK tare da mambobin rundunar tabbatar da tsaro da kuma jami’an sa-kai na Civilian JTF sun kakkabe maboyar ’yan ta’adda a Mar, Subdu, Yaro Lawanti, da Yaro Shuwari, da ma sauran yankunan da ke kusa da dajin Bulabulin da kuma yankin Kamadogu Yobe."
“Yayin gudanar da aikin, tare da tallafin jiragen yaƙi na sojojin sama, dakarun sun yi taho-mu-gama da ’yan ta’adda a ƙauyen Malam Shiri inda suka yi amfani da dabarun yaƙi na kewaye maharan, inda suka kashe ’yan ta’adda 11 tare da tilasta wa sauran tserewa da raunuka daban-daban."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi aika aika a Adamawa, Gwamna Fintiri ya sha alwashi

- Laftanar Kanal Sani Uba

Dakarun Sojoji sun kwato makamai

A cewarsa, an lalata dukkan wuraren da maharan ke dogaro da su don rayuwa, kuma binciken wurin ya kai ga ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda 9, bindigun harbo jirage na PKT guda uku, babura 5, dumbin alburusai, da kayayyakin da ake amfani da su wajen haɗa bama-bamai.

Ya kuma lura cewa, hakanan a yankin Timbuktu da ke kan hanyar Wajiroko zuwa Sabongari, dakarun sun ƙara yin artabu da ’yan ta’adda tare da tallafin sashen sojojin sama na OPHK.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda
Makaman da sojoji suka kwato a hannun 'yan ta'adda a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'adda

“Dakarun cikin jajircewa da kiyaye dabarun yaƙi, sun tsaya a matsayinsu inda suka yi maganin ’yan ta’addan yadda ya kamata."
"Binciken da aka yi bayan hakan ya nuna an kashe ’yan ta’adda bakwai tare da alamun jini da sassan jiki da ke nuna cewa an samu ƙarin asarar rayuka masu yawa a ɓangaren maƙiya a lokacin harin "

- Laftanar Kanal Sani Uba

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Najeriya suka ki karbar cin hancin N100m

Ya lissafa kayayyakin da aka ƙwato waɗanda suka haɗa da bindigogin AK-47, RPG, dumbin alburusai da kayayyakin sadarwa.

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakaru sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP da ke kai hare-hare.

Sojojin sun kuma samu nasarar kashe wani babban kwamanda da aka bayyana sunansa da Abu Umar Bundi Munzir tare da wasu ‘yan ta'adda 24 a jihar Borno.

Nasarar sojojin ta biyo bayan dakile wani harin haɗin gwiwa da aka kai wa kauyen Kukareta da ke Borno da dakarun Operation Hadin Kai suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng