Gwamna Abba Kabir Ya Gano Yan Siyasar da ke Rura Wutar Matsalar Tsaro a Najeriya
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya zargi wasu yan siyasa da amfani da matsalar tsaron Najeriya domin cimma burinsu
- Abba Gida-Gida ya ce wasu mutane marasa kishin kasa ke rura matsalar tsaro, wanda hakan ke kawo cikas ga kokarin samar da tsaro a kasar nan
- Ya bayyana cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin tsare rayukan al'umma a fadin jihar Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi zargin cewa wasu mutane na amfani da matsalolin tsaro a Najeriya domin cimma muradunsu na siyasa.
Abba ya bayyana hakan ne a wani taron kasa da aka gudanar a Lagos, inda ya ce Najeriya na fuskantar manyan kalubalen tsaro da ke bukatar hadin kai tsakanin gwamnati da al’umma.

Source: Facebook
Ya ce tsaro ba alhakin gwamnati kadai ba ne, akwai bukatar hada kai da jama’a gaba daya wajen magance duk wani kalubale, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Gwamna Abba ya zargi yan siya
Gwamnan na Kano ya ce abin takaici ne yadda wasu 'yan siyasa marasa kishin kasa ke amfani da matsalolin tsaro domin cin riba ta siyasa.
Ya kara da cewa hakan na kawo cikas ga kokarin gwamnati, musamman na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wajen magance matsalar tsaro a fadin kasar nan.
Abbba Gida-Gida ya ce Kano na fuskantar matsaloli irin su rikicin ‘yan daba da satar wayoyi, sai kuma wasu ‘yan bindiga daga jihar Katsina da suka shiga wasu kananan hukumomi kamar Tsanyawa, Shanono da Ghari.
Matakan da gwamnatin Abba ta dauka
Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai cikin gaggawa domin dakile barazanar, in da ya ce suna aiki tare da jami’an tsaro kamar sojoji, ‘yan sanda da DSS domin hana ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.

Kara karanta wannan
Mutanen jihar Kano na cikin alheri a mulkin Tinubu, an raba wa talakawa Naira biliyan 48
Haka kuma, ya ce sun kafa rundunar sa-kai domin taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da matsalar tsaro a fadin kananan hukumomin da matsalar ta shafa a Kano.
Najeriya na fuskantar rabuwar kai
Gwamnan ya yi gargadin cewa rabuwar kai na kara bayyana a Najeriya, yan mai cewa hakan na fitowa fili ta hanyar rashin tsaro, matsin tattalin arziki da kuma raguwar amincewar jama’a ga gwamnati.
Abba Kabir ya ce gwamnatin Kano ta mayar da hankali wajen samar da adalci, hada kai da walwalar jama’a domin samar da zaman lafiya, cewar Daily Post.

Source: Facebook
Ya kara da cewa sun bullo da tsare-tsare domin kare hakkin jama’a da inganta aikin ‘yan sanda, ciki har da samar da lauyoyi ga wadanda ake tuhuma da kuma hana kamue ba bisa ka’ida ba.
An kama mai taimakon yan bindiga a Kano
A wani labarin, kun ji cewa jami'an hukumar DSS sun kama wata mata mai shekaru 25 da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga harsasai a Kano.
Jami'an sun kama ta da zargin safarar harsasai da ta ke amso wa daga wata jihar domin kai wa ‘yan bindiga da ke addabar jihohi daban-daban a Arewa.
Yayin gudanar da bincike, matar ta amsa cewa ta shafe watanni biyu tana wannan haramtacciyar sana’a ta safarar makamai da harsasai ga masu aikata laifuffuka.
Asali: Legit.ng
