Gwamna Abba Ya Dauko Batun Nada Garo Mataimakinsa, Ya Fadi Dalilin Ba Shi Mukami

Gwamna Abba Ya Dauko Batun Nada Garo Mataimakinsa, Ya Fadi Dalilin Ba Shi Mukami

  • Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kare matakin da ya dauka na nada Hon. Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa
  • Kalaman nasa na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da nadin da aka yi wa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna
  • Gwamna Abba ya bayyana cewa Murtala Sule Garo ya cancanci mukamin da aka ba shi domin mutum ne da zai iya ba da gudunmawar da ta dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan nada Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Zulum ya yi abin mamaki, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Gwamna Abba ya bayyana cewa nadawa da tabbatar da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamna ya ginu ne bisa kwarewarsa da jajircewarsa ga ci gaban jihar.

Gwamna Abba ya magantu kan nadin Murtala Sule Garo
Murtala Sule Garo da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Murtala Sule Garo, Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Mustapha Muhammad ya fitar, wadda aka ba da kwafinta ga jaridar The Punch ranar Laraba, 29 ga watan Afirilun 2026.

Me Abba ya ce kan nadin Murtala Garo?

A cewar sanarwar, Gwamna Abba ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron majalisar zartarwa karo na 39 da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026.

“Mun yi ƙoƙari sosai wajen zaɓar wanda zai iya ba da gudummawar da ta dace wajen ci gaban jihar,” in ji gwamnan kamar yadda aka ambato shi a cikin sanarwar.

Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne Gwamna Abba ya aika da sunan Murtala Sule Garo zuwa majalisar dokoki ta jihar domin tantancewa biyo bayan murabus ɗin tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Kara karanta wannan

"Abba ne jagora a Kano": Ganduje ya yi magana kan naɗa Garo mataimakin gwamna

Gwamnan ya bayyana cewa:

“An gabatar da sunayen mutane da dama, amma dole ne mu duba ayyukansu na baya, mu duba ƙwarewarsu."
"Mu duba abin da suka yi wa jihar a baya da kuma abin da za su iya bayarwa a yau; Murtala Sule Garo gogaggen ɗan siyasa ne wanda zai iya ba da tasa gudummawar.”

Gwamna Abba ya yaba wa Majalisar Kano

Haka kuma Gwamna Abba ya jinjinawa majalisar dokokin jihar, ƙarƙashin jagorancin Shugaban majalisa, Jibril Ismail Falgore, bisa gaggauta tabbatar da wanda aka naɗa, rahoton jaridar PM News ya tabbatar da hakan.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a rantsar da sabon mataimakin gwamnan da aka tabbatar, sannan ya yi kira ga jama’a da su ba shi goyon baya domin ya sauke nauyin da aka ɗora masa yadda ya kamata.

Gwamna Abba ya fadi dalilin nada Murtala Sule Garo mataimakin gwamna
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taron shigarsa jam'iyyar APC Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamna Abba ya taya Maimota murna

Kara karanta wannan

Gwamnan Legas ya bi sahu, ya nuna wanda yake goyon bayan ya gaje shi a zaben 2027

Yayin da yake taya Garo murnar samun nasarar tsallake tantancewar majalisa, ya kuma taya murna ga sabuwar shugabar ma’aikatan jiha, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota.

Gwamnan ya ce gudummawar Maimota lokacin tana matsayin Darakta da kuma babbar sakatariya ba za a iya mantawa da ita ba.

Ya buƙaci masu ruwa da tsaki da ma’aikatan gwamnati da su marawa bayanta don tabbatar da nasararta a wannan sabon matsayi.

Gwamnan Kano ya magantu kan nuna dan kamfai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan nuna dan kamfai da wasu mata suka rika yi.

Gwamna Abba ya bayyana cewa ba shi da hannu a zargin da ke yawo na cewa gwamnatinsa ta raba dan kamfai ga mata a matsayin tallafi.

Hakazalika, gwamnan ya bayyana cewa bai san da abin da ya faru ba, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da ya sabawa al’ada da addini.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng