Mummunar Gobara Ta Tashi a Kano, 'Yan Kasuwa Sun Yi Asarar Miliyoyin Naira
- Wata gobara da ta tashi a sanyin safiyar ranar Laraba ta kone wasu sassan wani babban bene da ke kan hanyar zuwa filin jirgin sama
- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da cewa gobarar ta lalata shaguna guda biyu wadanda ke makare da kayayyakin asibiti
- Jami'an kwana-kwana sun yi nasarar shawo kan wutar bayan an tura motocin kashe gobarar daga kasuwar Abubakar Rimi da wurare uku
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano – Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayar da rahoton afkuwar wata mummunar gobara a lamba 20A kan hanyar filin jirgin sama da ke karamar hukumar Fagge.
Gobarar ta shafi wani bene mai hawa biyu wanda ake amfani da shi wajen harkokin kasuwanci, kuma an ce 'yan kasuwar wajen sun tafka asara mai yawa.

Kara karanta wannan
Trump ya ki amince wa da wani bangare a sabon tayin sulhu da Iran ta yi wa Amurka

Source: UGC
Gobara ta tashi a wasu shaguna a Kano
Bayani game da tashin gobarar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya fitar, a cewar rahoton Punch.
Saminu Yusif ya sanar da cewa sashen karbar korafe-korafen gaggawa ya karbi kiran waya daga wani mutum mai suna Chukude, wanda ya sanar da su tashin gobarar a yayin da dare ya tsala.
Hukumar ta tura jami’an kwana-kwana daga babban ofishinta da sauran ofisoshi da ke cikin birnin domin shawo kan lamarin.
"Bayan an samu wannan kira, an tura jami'an kashe gobara daga hedikwatar hukumar da sauran ofisoshi da ke cikin kwaryar jihar domin kai daukin gaggawa."
- Saminu Yusif Abdullahi.
Yadda ka tura motocin kwana kwana daga
Don ganin an kashe wutar cikin sauri, hukumar ta sanar da cewa ta tura manyan motocin kashe gobara daga:
- Kasuwar Abubakar Rimi
- Kasuwar Kantin Kwari
- Tashar Bompai
- Babban ofishin kashe gobara na cikin birni
Jami'an sun iske wutar ta riga ta kama ginin, inda shagunan kayan asibiti guda biyu da ke can kasan ginin suka kone kurmus, in ji rahoton Daily Post.

Source: Facebook
Jan hankali daga hukuma
Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Sani Anas, ya bukaci mazauna jihar da su kara kiyayewa tare da daukar matakan kariya domin kauce wa afkuwar gobara.
Ya kuma ba da shawara cewa duk lokacin da aka samu wani yanayi na gaggawa, mutane su hanzarta sanar da hukumomin da suka dace a kan lokaci.
A halin yanzu, hukumar na ci gaba da gudanar da bincike domin gano takamaiman dalilin da ya janyo tashin wannan gobara da irin asarar da aka yi.
Gobara ta tashi a kasuwar Kano
A wani labari, mun ruwaito cewa, an shiga halin jimami a Kano biyo bayan tashin wata mummunar gobara a daya daga cikin fitattun kasuwannin da ake da su.
Mummunar gobarar dai ta tashi ne da sanyin Asuba inda ta lakume shagunan 'yan kasuwa da dama wadanda adadinsu ya wuce 40.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gobarar na ci gaba da ci a kasuwar yayin da ake jiran jami'an hukumar kashe gobara ta Kano su kawo daukin gaggawa.
Asali: Legit.ng
