'Yan Bindiga Sun Nuna Tsaurin Ido, Sun Yi gaba da gaba da Sojoji, An Rasa Rayuka
- Wasu 'yan bindiga sun buɗe wa ayarin motocin sojojin ƙasar Ghana wuta a yankin Binduri da ke Arewa maso gabashin ƙasar, inda suka kashe farar hula
- Rundunar sojin ƙasar ta bayyana cewa dakarunta sun mayar da martani inda suka kashe mahara bakwai, tare da kama wasu mutane 10
- Yankin Bawku ya daɗe yana fama da rikice-rikice, lamarin da ya sa gwamnati girke sojoji na musamman domin kare iyakokin ƙasar da ba matafiya kariya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ghana – Wani farmaki da wasu 'yan bindiga suka kai wa ayarin sojojin ƙasar Ghana ya yi sanadin mutuwar farar hula uku a safiyar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026.
Rundunar sojin ƙasar ta tabbatar da cewa ayarin, wanda ke rakiyar farar hula kusan 140 daga garin Bawku zuwa Bolgatanga, ya faɗa cikin harin kwantan ɓauna a yankin Binduri.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun farmaki ayarin sojojin Ghana
A cikin wata sanarwa da BBC ta gani a ranar Talata, rundunar sojojin Ghana ta bayyana cewa:
“An buɗe wa ayarin motocin sojojin Ghana wuta a safiyar Litinin yayin da suke ba farar hula 140 kariya. Wannan ya yi sanadin mutuwar mutane uku da kuma raunata mutum ɗaya.”
Jami’an sojin da ke rakiyar ayarin sun mayar da martani cikin gaggawa inda suka fatattaki maharan. A yayin fafatawar, sojojin sun yi nasarar kashe bakwai daga cikin 'yan ta'addar.
Haka kuma, rundunar ta gudanar da bincike na musamman inda ta gano makamai a hannun ɗaya daga cikin maharan da ya tsere ya fake a cikin wani masallaci.
Sojoji sun yi kame a kasar Ghana
Sojojin sun gano bindiga ƙirar G3 automatic, gidajen harsasai masu jigida guda biyu maƙil da harsasai, da kuma ƙarin wasu harsasai guda 176.
Kazalika, an kama wasu mutane 10 da ake zargi waɗanda yanzu haka suke taimaka wa jami'an tsaro wajen gudanar da bincike.
Rundunar sojin ta gargaɗi jama'a da su daina tsoma baki a ayyukan tsaro, inda ta buƙaci haɗin kai domin tabbatar da doka da oda.

Source: Getty Images
Matakin da rundunar sojoji ta dauka
Gwamnati ta sanya dokar ta-ɓaci tare da kuma gudanar da sintiri na haɗin gwiwa tsakanin sojoji da ƴan sanda domin dakile tashe-tashen hankula a yankin.
Rahoton The Cable ya nuna cewa sojojin da aka girke a yankin suna da nauyin kare iyakokin ƙasar da ƙasar Burkina Faso.
Rundunar sojin ta miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan harin, tare da alwashin ci gaba da kakkabe 'yan ta'adda.
Mutane sun mutu wurin shiga aikin soja
A wani labari, mun ruwaito cewa akalla mutane shida sun mutu sakamakon cunkoson matasa da aka samu a wajen daukar sojoji a babban birnin Ghana.
An rahoto cewa an yi turmutsutsun ne a yayin shirin daukar sojoji da aka gudanar a filin wasan El-Wak Sports Stadium da ke Accra, babban birnin kasar.
A cikin wata sanarwa ta biyu da rundunar sojin ta fitar, Gwamnatin kasar Ghana ta yanke shawarar dakatar da shirin daukar sababbin sojoji don tantance abin da ya faru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

