Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Rikakken Jagoran 'Yan Bindiga

Dubu Ta Cika: 'Yan Sanda Sun Cafke Rikakken Jagoran 'Yan Bindiga

  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarori a yakin da take yi da 'yan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka
  • Jami'an rundunar 'yan sandan sun samu nasarar cafke wani tantirin jagoran 'yan bindiga a karamar hukumar Kaura Namoda
  • Hakazalika, jami'an 'yan sandan sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargi da laifin gudanar da sana'ar sayar da ganyen tabar wiwi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da 'yan bindiga da manyan laifuffuka.

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ta cafke wani da ake zargi jagoran 'yan bindiga ne tare da ƙwato makamai, miyagun ƙwayoyi, da kuma kayayyakin sata a faɗin jihar.

'Yan sanda sun cafke jagoran 'yan bindiga a Zamfara
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce jami’in yaɗa labarai na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, 29 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda a Borno, an yi masu gagarumar barna

'Yan sanda sun cafke jagoran 'yan bindiga

Kakakin 'yan sandan ya ce an samu waɗannan nasarori ne tsakanin mako guda da kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmad Muhammad Bello, ya kama aiki.

Ya lura cewa waɗannan ayyuka wani ɓangare ne na sabon ƙoƙari na dawo da tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyi a cikin jihar, rahoton Radio Nigeria Kaduna ya tabbatar da hakan.

Rundunar ta sanar da kama wani da ake zargi jagoran 'yan bindiga ne, Audu Maikano, yayin wani samame na haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro a ƙauyen Dan-Makulu, da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda.

“Jami’an ƴan sanda ne suka gudanar da aikin tare da haɗin gwiwar sojoji, biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan wata ƙungiya da ke addabar mazauna yankin, musamman a kan hanyoyin da suka haɗa Kaura Namoda da Kasuwar Daji."
“Abubuwan da aka ƙwato daga hannun wanda ake zargin sun haɗa da bindiga kirar AK-47 da aka ƙera da hannu, alburusai, bindigun gargajiya, adduna, layu, da wayoyin hannu da dama."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi aika aika a Adamawa, Gwamna Fintiri ya sha alwashi

"Ƴan sanda na ci gaba da bincike don kamo sauran mambobin ƙungiyar."

- DSP Yazid Abubakar

An kama masu sayar da wiwi

Jami’in yaɗa labaran ya bayyana cewa a wani samame na daban, an kama mutane biyu a Gusau bisa zargin mallakar ganyen da ake zargin tabar wiwi ne.

An bayar da rahoton cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin gudanar da sana’ar sayar da ganyen.

Bugu da ƙari, ƴan sanda sun kai samame wata maboyar masu shan ƙwayoyi a yankin Gangaren Gulbi, inda suka ƙwato kwalaben kodin, hodar roba da sauran abubuwan da suka shafi shaye-shaye.

'Yan sanda sun cafke masu aikata laifuffuka a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An cafke masu ganganci da babura

Rundunar ta kuma tabbatar da kama wasu mutane uku da ke da alaƙa da ayyukan ƙungiyar “Yan Arlit”, waɗanda aka sani da guje-guje da babura ba tare da kiyayewa ba da kuma tayar da hankalin jama’a.

An ƙwato abubuwa da suka haɗa da ganyen da ake zargin wiwi ne, bututun shakar ƙwayoyi, wuƙa, da babura da dama.

Rundunar ta jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka domin kamo sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Najeriya suka ki karbar cin hancin N100m

'Yan bindiga sun kashe fasto

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari wurin wani taron wa'azi inda suka hallaka fasto tare da sace mutane da dama a jihar Ekiti.

Maharan sun mamaye filin taron ne a lokacin da ake tsaka da gudanar da wa’azi, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Majiyoyi sun bayyana cewa miyagun maharan sun zo ne a ayari kuma suna dauke da mugayen makamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng