Kotu Ta amince da Bukatar Gwamnatin Tinubu a Shari'ar Mutane 6 da Ake Zargi da Shirin Juyin Mulki
- Gwamnatin tarayyya ta fara gabatar da shaidu a gaban babbar kotun tarayya kan wadanda ake zargi da kitsa juyin mulki
- A zaman da kotu ta yi ranar Laraba, lauyan gwamnati ya bukaci a boye bayanan shaidu domin kare su daga yiwuwar shiga matsala
- Alkalin kotun, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da wannan bukatar duk da an dan samu takaddama daga bangaren wadanda ake zargi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja – Babbar Kotun Tarayya, Abuja ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na boye suna da asalin wata shaida daga rundunar sojojin Najeriya a shari’ar da ake yi wa mutane shida da ake zargi da yunkurin juyin mulki.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke wannan hukunci bayan sauraron hujjojin lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo (SAN), da kuma lauyoyin masu kare wadanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan
Shaidan sojoji ya fasa kwai a kotu, ya fadi yadda aka shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Source: Twitter
Vanguard ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta shigar da tuhume-tuhume guda 13 kan wadanda ake zargin a kara mai lamba FHC/ABJ/CR/206/2026.
Sunayen wadanda ake tuhuma da juyin-mulki
Wadanda ake zargin sun hada da tsohon Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana, tsohon Kyaftin (NN) Erasmus Ochegobia Victor, Sufeto Ahmed Ibrahim, Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani.
Ko da yake tsohon Karamin ministan albarkatun mai, Timipre Sylva, ba a sanya shi cikin wadanda ake tuhuma ba, amma an bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
An tuhumi wadanda ake zargin da aikata laifuffuka da suka hada da cin amanar kasa da ta’addanci, ciki har da kin bayar da bayanan sirri na tsaro da karbar kudade da ake zargin suna da alaka da daukar nauyin ta’addanci.
Shaidu uku daga Jaiz Bank, SunTrust Bank da Providus Bank sun gabatar da bayanansu, kuma kotu ta karbe su a matsayin hujjoji.
Yadda aka yi takaddama a kotu
Lokacin da aka kira shaida ta hudu, Oyedepo ya roki kotu da a boye suna da asalin shaidar domin kare shi daga barazana, yana mai kafa hujja da sashe na 232 na dokar ACJA ta shekarar 2015.
Lauyoyin wadanda ake tuhuma ba su yi adawa da bukatar ba, amma sun dage cewa dole ne su san ainihin shaidar domin tabbatar da adalci.
Sun bayyana cewa boye shaida daga jama’a na iya zama daidai, amma boye ta gaba daya daga bangaren kare kai zai hana yin cikakken bincike kan sahihancin shaidar.
Sun kuma jaddada cewa dokar ba ta hana sanin ainihin shaida a cikin shari’a ba, duk da cewa tana bada damar daukar matakan kariya.

Source: Getty Images
Hukuncin kotu kan bukatar gwamnati
Da take yanke hukunci, Mai shari’a Abdulmalik ta ce bukatar gwamnatin ta dace, musamman ganin cewa daya daga cikin tuhume-tuhumen ya shafi ta’addanci.
Ta ce doka ta ba kotu damar daukar matakan kariya, ciki har da boye suna, adireshi da bayanan tuntuba idan akwai dalilan tsaro, in ji rahoton Leadership.
Saboda haka, kotu ta amince da bukatar tare da umartar cewa kada a bayyana sunan shaidar a cikin takardun kotu ko bayanan shari’a.
Sojoji sun gabatar da shaida a kotu
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta yi bayanin yadda aka gano shirin kifar da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayin gabatar da shaida a kotu.
Shaidan ya ce binciken ya fara ne bayan rahoton sirri da shugaban rundunar soji, Janar O. O. Oluyede, ya samu kan wani shiri na kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Ya ce an kama Kanal M. A. Ma’aji, inda aka kwace wayarsa da wasu kayayyaki, haka kuma an gano wani littafi dauke da bayanai masu muhimmanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

