Kurunkus: Kotun Koli Ta Sanya Lokacin Yanke Hukunci kan Takaddamar Shugabancin ADC

Kurunkus: Kotun Koli Ta Sanya Lokacin Yanke Hukunci kan Takaddamar Shugabancin ADC

  • Jam'iyyyar ADC ta tsinci kanta cikin rikicin shugabanci wanda ya sanya shari'a ta kai har zuwa ga Kotun Kolin Najeriya
  • Kotun Koli ta sanya lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar wadda ta shafi bangaren David Mark da Nafiu Bala Gombe
  • Tun da farko dai bangaren David Mark ya bukaci kotun da ta yanke hukunci kan shari'ar domin kada hakan ya jawo masu matsala

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kotun Ƙoli ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan takaddamar rikicin shugabanci na jam'iyyar ADC.

Kotun Koli ta tsayar da ranar Alhamis, 30 ga Afrilun 2026, domin yanke hukunci a kan takaddamar shugabanci da ke addabar babbar jam’iyyar adawa ADC.

Kotun Koli za ta yanke hukunci kan rikicin ADC
David Mark da Rauf Aregbesola a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @ADCVanguard
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton tsayar da ranar da Kotun Kolin ta yi a ranar Laraba, 29 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Kotu ta rikita lissafin 'yan adawa, ta hana INEC amincewa da tarukan jam'iyyar ADC

Kotun ƙolin dai ta tanadi hukuncin ne tun farko, lamarin da ya sa jam’iyyar adawar shigar da koken neman agaji ga babbar alƙalin Najeriya (CJN) cewa lokaci yana ƙure masu.

Yaushe Kotun Koli za ta yanke hukunci?

Sai dai a ranar Laraba, 29 ga watan Afirilun 2026, Kotun Kolin ta sanar da cewa za a sanar da hukuncin da misalin ƙarfe 2:00 na ranar Alhamis, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Wani kwamitin alƙalai biyar na Kotun Kolin, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Mohammed Garba, ya tsayar da ranar yanke hukuncin ne bayan da ɓangarorin biyu suka gabatar da bayanan karshe na kariya.

Jam'iyyar ADC na fama da rikicin shugabanci

David Mark, wanda ke jagorantar wani bangare na jam’iyyar, yana ƙalubalantar hukuncin ranar 12 ga Maris na kotun daukaka kara, wanda ya umarci ɓangarorin da su ci gaba da kasancewa yadda suke a cikin takaddamar.

A cikin daukaka ƙarar tasa, tsohon shugaban majalisar dattawan ya kafa hujjar cewa kotun ɗaukaka ƙarar ta zarce huruminta, inda ya dage cewa rikicin ya shafi cikin gidan jam’iyya ne, wanda kotuna ba su da ikon shiga tsakani.

Kara karanta wannan

2027: Shugaba Tinubu ya karbi fom din neman sake tsayawa takara a inuwar APC

Wasu mambobin jam’iyyar da ba sa jin daɗin yadda ake gudanar da harkokin ne suka shigar da ƙarar, ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe, wanda ke ƙalubalantar halaccin shugabancin David Mark a jam’iyyar.

Kotun Koli za ta yanke hukunci kan rikicin ADC
Aminu Waziri Tambuwal, Peter Obi da Atiku Abubakar a wajen taron ADC Hoto: @atiku
Source: Twitter

An shigar da jagororin jam'iyyar ADC kara

Sauran waɗanda ake ƙara a cikin ɗaukaka ƙarar sun haɗa da jam’iyyar ADC, sakatarenta na kasa, Rauf Aregbesola, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da kuma tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Ralph Nwosu.

Haka kuma David Mark yana neman umarnin hana INEC amincewa da kowane shugabanci in ban da nasa bangaren, har sai an yanke hukuncin ɗaukaka ƙarar.

Sai dai, waɗanda ake ƙara sun buƙaci Kotun Kolin da ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar, suna masu cewa ƙaramar kotun ta bi tsari yadda ya kamata wajen sauraron maganar.

Kotu ta ba INEC umarni kan ADC

A wani labarin kuma kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba hukumar zabe ta INEC kan jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Taba mutuncin Sarkin Musulmin Najeriya da Matawalle ya jefa 'yar majalisar Amurka a matsala

Babbar kotun ta hana INEC amincewa ko shiga duk wani taro da shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar ADC suka shirya a matakin kasa da jihohi.

Wadanda suka shigar da kara sun ce shugabancin rikon kwarya da aka nada karkashin jagorancin Sanata David Mark, ba shi da hurumin gudanar da tarukan jihohi ko kafa kwamitin da zai yi hakan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng