Manyan Labarai A Yau
Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta cafke mutum shida da take zargi da hannu a kisan gillan da aka yi wa wass bayin Allah matafiya a kusa da Mafaban Jos.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni ga hukumar ICPC kan ma'aikatar bogi. Shugaba Tinubu ya umarci a gudanar da bincike tare da kawo masa rahoto.
ICPC ta zargi Nasir El-Rufai da karya sharudan ziyarar asibiti da kotu ta amince masa, tare da kama likitansa Farfesa Bello Abubakar domin bincike.
Hukumar Kashe Gobara ta Kano ta ce gobara 30 ta kashe mutane biyar tare da lalata dukiyar Naira miliyan 120 a watan Yuni, yayin da ta ceto dukiyar miliyan 481.
Wasu manyan kwamandoji a kungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun mika wiya ga dakarun sojojin Najeriya. Dakarun sojojin sun samu muhimman bayanai a hannunsu.
Hukumar NIS ta fitar da sabon tsarin sabunta fasfo ga 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, tare da bayyana matakan amfani da tsarin kai-da-kai cikin sauki.
An fara gudanar da jana'izar tsohon jagoran addini na kasar Iran, marigayi Ayatollah Ali Khemenei. Za a kwashe ana jana'izar Khamenei a wurare daban-daban.
Gwamnatin jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta sanya dokar hana fita a wasu garuruwa biyo bayan barkewar rikicin kabilanci da ya jawo asarar rayuka.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya yi barazanar kai shugaban ma'aikatar bogi, Adeniyi Adeyemi, kara gaban kotu kan zargin bata suna.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari