Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Kuri'un da Tinubu Zai Samu a Kaduna a Zaben 2027
- Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi hasashen kuri'un da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai samu a jiharsa a zaben 2027
- Sanata Uba Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai samu kuri'u masu kyau a Kaduna saboda ayyukan da ya aiwatar
- Gwamnan ya bayyana cewa shugaban kasar da jam'iyyar APC ba su da wata adawa a jihar Kaduna saboda jama'a na goyon bayansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana kuri'un da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, zai samu a jihar a zaben 2027 da ake tunkara.
Gwamna Uba Sani ya nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai samu akalla kashi 70 cikin ɗari na ƙuri’un jihar a lokacin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ranar Talata, 28 ga watan Afirilun 2026 lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin tawagar yaɗa labaran shugaban ƙasa.
Meyasa Uba Sani ya yi hasashe kan Tinubu?
Gwamna Uba Sani ya danganta hasashen nasa ga abin da ya bayyana a matsayin rawar gani da shugaban kasar yake takawa a kan mulki, wanda ya ce hakan ya gamsar da mutanen jihar.
Uba Sani ya bayyana cewa, ko da yake sakamakon da ake gani a kafofin sada zumunta na iya kasancewa daban, shugaban kasar zai samu gagarumin goyon baya lokacin da aka kaɗa ƙuri’u a zahiri a faɗin ƙasar.
Ya ci gaba da cewa babu wata babbar adawa ga shugaban ƙasar ko jam’iyyar APC a jihar Kaduna, yana mai nuni da tallafin gwamnatin tarayya da ayyukan raya ƙasa da ake ci gaba da yi, The Punch ta dauko labarin.
Uba Sani ya yabawa Tinubu
Yayin da yake duba tarihin siyasar Tinubu, gwamnan ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen ɗan kishin tsarin mulki kuma tsohon ɗan fafutuka, yayin da ya soki jiga-jigan ’yan adawa waɗanda ya zarga da ƙoƙarin yi wa tsarin dimokuraidyya na Najeriya zagon ƙasa.
Gwamnan ya kuma kafa hujjar cewa gwamnatin Tinubu ta yi wa Arewacin Najeriya ayyukan da babu wata gwamnati da ta gabace ta da ta yi, inda ya nuna amincewar da aka yi kwanan nan na manyan ayyukan layin dogo da hanyoyi na biliyoyin naira a jihar Kaduna.
A cewarsa, ana sa ran waɗannan ayyuka za su bunƙasa ababen more rayuwa tare da haɓaka tattalin arziƙi a yankin idan an kammala su.

Source: Twitter
Gwamna Uba Sani ya kuma yaba wa gwamnatin bisa ƙara raba kuɗaɗe ga gwamnatocin jihohi, wanda ya ce hakan ya bai wa jihohin damar kai ayyukan raya ƙasa zuwa ga al’ummomin karkara.
Ya ƙara da cewa ingantaccen haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi ya inganta harkar shugabanci da ayyukan jin daɗin jama’a, wanda hakan ya taimaka wajen samun goyon bayan jama’a ga shugaban kasar.
Tinubu ya goyi bayan Hamzat
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana wanda yake son ya zama gwamnan jihar Legas karkashin inuwar APC a zaben 2027.
Shugaba Tinubu ya amince tare da goyon bayan Obafemi Hamzat a matsayin 'dan takarar gwamnan APC a zaben gwamnan Legas na shekarar 2027.
Mai girma Tinibj ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Majalisar dattawan APC mai ba da shawara kan harkokin mulkin jihar Legas (GAC).
Asali: Legit.ng

