Kwana 1 bayan Sayen Fom din N50m, Mai Neman Takarar Gwamna a APC Ya Janye, Ya Fadi Dalili

Kwana 1 bayan Sayen Fom din N50m, Mai Neman Takarar Gwamna a APC Ya Janye, Ya Fadi Dalili

  • Daya daga cikin manya a cikin jam'iyyar APC, Abdul-Azeez Adeniran, ya sanar da matsayarsa dangane da neman takarar gwamnan jihar Legas
  • Abdul-Azeez Adeniran wanda aka fi sani da Jandor ya bayyana cewa ya janye daga neman takarar gwamnan Legas karkashin inuwar APC
  • Janyewarsa dai na zuwa ne bayan APC da Shugaba Bola Tinubu sun amince da Obafemi Hamzat a matsayin dan takarar gwamna na APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Wani jigo a jam’iyyar APC, Abdul-Azeez Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya janye daga takarar neman gwamnan jihar Legas.

Shawarar Adediran ta biyo bayan amincewa da mataimakin gwamnan jihar, Obafemi Hamzat, a matsayin ɗan takarar gwamnan APC na bai-ɗaya.

Jandor ya goyi bayan zabin Tinubu kan takarar gwamnan Legas
Abdul-Azeez Adeniran bayan ya sayi fom din neman takarar gwamnan Legas a karkashin APC Hoto: @officialjandor
Source: Twitter

Abdul-Azeez Adediran ya sanar da janyewarsa ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Mai son takarar gwamna a APC ya ki yarda da zabin Tinubu, ya yi barazanar zuwa kotu

Janyewarsa na zuwa ne dai bayan ya saya fom din na gani ina so da na neman takarar gwamnan Legas a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Meyasa Jandor ya janye takarar gwamna?

Jandor ya bayyana cewa janyewarsa na zuwa ne bayan amincewa da Dr. Kadiri Obafemi Hamzat, a matsayin dan takarar gwamnan APC na Legas.

“Biyo bayan amincewa da Dr. Kadiri Hamzat da shugabanmu, shugaban Najeriya, da shugabannin jam’iyyarmu na Legas suka yi, kuma sakamakon la’akari da yanayin siyasa da ake ciki a babbar jam’iyyarmu, na yanke shawarar janyewa daga takarar gwamnan jihar Legas ta 2027."
“Wannan shawara ba ta samo asali ne daga rauni ko rashin ƙwarewa ba, a’a, na yi hakan ne domin nuna ƙarfi, tarbiyya, da kuma girmama haɗin kai da kasancewar jam’iyyar tsintsiya madaurinki ɗaya."
“Bari na fayyace wannan, na ci gaba da kasancewa mamba mai aminci da biyayya ga APC. Haka kuma ina jaddada cikakkiyar biyayyata da girmamawa ga shugaban kasa kuma shugaban jam’iyyarmu na ƙasa, Mai girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR."
“Shugabancinsa shi ne ginshiƙin daidaito da ci gaban jam’iyyarmu da ma ƙasa baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya zabi wanda yake so ya gaji kujerar gwamnan Legas a zaben 2027

- Abdul-Azeez Adeniran

Jandor zai marawa jam'iyyar APC baya

Ya ce zai marawa shawarar jam’iyyar baya, sannan ya ƙarfafa gwiwar magoya bayansa da su yi hakan.

Adediran ya kuma bayyana cewa yana Abuja ranar Laraba, inda Shugaba Bola Tinubu ya yanke wannan shawara.

Jandor ya saya fom din neman takarar gwamnan Legas karkashin APC
Abdul-Azeez Adeniran da fom din neman takarar gwamnan Legas karkashin APC Hoto: @officialjandor
Source: Twitter
“Bisa wannan dalili, na amince 100 bisa 100 da matsaya da alkiblar da shugaban kasa ya dauja game da tsarin takarar gwamnan jihar Legas."
"Fifita jam’iyya da haɗa kai cikin dabarun yaƙi suna da mahimmanci wajen dorewar nasarorin da muka gina tare cikin shekaru."

- Abdul-Azeez Adeniran

Mai son takara ya yi barazanar zuwa kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai neman takarar gwamnan jihar Legas a karkashin inuwar APC, Samuel Ajose, ya musanta goyon bayan Obafemi Hamzat.

Samuel Ajose ya karyata sanarwar da ke nuna cewa ya amince da Obafemi Hamzat a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar.

Hakazalika, ya yi barazanar daukar matakin shari'a kan masu yada sanarwar, inda ya bukaci su gaggauta cire ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng