Legas da Jihohin Arewa 2 Za Su Amfana da Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Ayyukan $2.99bn

Legas da Jihohin Arewa 2 Za Su Amfana da Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Ayyukan $2.99bn

  • Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da makudan kudade domin gudanar da manyan ayyukan layin dogo a jihohi uku
  • Ministan kudi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da $2.99bn domin gudanar da ayyukan a jihohin Kano, Kaduna da Legas
  • Taiwo Oyedele ya bayyana cewa amincewar ta yi daidai da kudirin gwamnatin tarayya na samar da ababen more rayuwa ga 'yan Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da kwangiloli na dala biliyan 2.99 domin manyan ayyukan layin dogo.

Majalisar zartarwa ta tarayyar ta amince da manyan ayyukan guda uku a jihohin Legas, Kano, da Kaduna.

FEC ta amince da ayyukan layin dogo a Kaduna, Kano da Legas
Mai girma Bola Tinubu na jagorantar taron FEC Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta ce Ministan kudi, Taiwo Oyedele, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan taron mako-mako na FEC a Abuja ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Masarautar Ilorin ta gano amfanin Tinubu a ofis, ta goyi bayan ya zarce zuwa 2031

Meyasa za a yi ayyukan layin dogo?

Taiwo Oyedele ya ce amincewar ta yi daidai da ƙudurin Gwamnatin tarayya na samar da ababen more rayuwa da ke kawo ci gaba ga ƙasa, haɓakar tattalin arziƙi, da inganta rayuwar jama'a.

Oyedele ya ƙara da cewa majalisar ta kuma kafa wani kwamiti na musamman na shugaban ƙasa kan fannin lantarki, wanda Shugaba Bola Tinubu zai jagoranta.

“Majalisar a yau ta amince da ba da kwangilolin ayyukan layin dogo guda uku masu kawo sauyi. Ɗaya shi ne aikin layin dogo na Green Line na Legas, a matakin farko."
“Na biyu shi ne aikin layin dogo na cikin birnin Kano. Na uku kuma shi ne aikin layin dogo na Kaduna."

- Taiwo Oyedele

A ina za a samo kudikin aikin dogon?

A cewarsa, ma’aikatar kuɗi ce za ta ɗauki nauyin ayyukan a madadin gwamnatin tarayya, tare da tallafin kuɗaɗe daga wasu hanyoyin.

Ministan ya ce ana ran waɗannan tsare-tsare guda uku za su inganta sufurin cikin birni sosai a manyan cibiyoyin tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tuna da mutanen da hare hare suka shafa a Plateau, ya ba da tallafin kudi

Oyedele ya bayyana Legas, Kano, da Kaduna a matsayin birane masu muhimmanci inda zuba jari a cikinsu zai iya samar da gagarumar riba, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Gwamnati za ta gudanar da ayyukan layin dogo
Ministan kudi, Taiwo Oyedele, na gaisawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter
“Waɗannan birane guda uku suna da muhimmanci da kima sosai. Dukkan birane suna da muhimmanci, amma waɗannan su ne wuraren da ƙoƙarin kashi 10 cikin 100 yake samar da sakamako na kashi 90 cikin 100.”

- Taiwo Oyedele

Ya ƙara da cewa layin dogo na Green Line yana ɗaya daga cikin ɓangarorin layin dogo na birnin Legas da aka fi jira a ga an aiwatar da shi.

Tinubu zai nada Ministan lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya zabo wanda yake so ya zama ministan da zai jagoranci ma'aikatar lantarki.

Shugaba Tinubu ya dauko Joseph Olasunkanmi Tegbe ya nada shi a matsayin Ministan lantaki bayan murabus din Adebayo Adelabu wanda ke son yin takarar gwamnan jihar Oyo.

Wannan zabi da shugaban kasar ya yi wa Joseph Tegbe na jiran tantancewa tare da amincewar majalisar dattawan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng