Trump Ya Kasa Hakura da Kalaman Shugaban Jamus, Ya Sake Yin Martani Mai Zafi
- Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya yi kalaman da ba su yi dadi ga Donald Trump ba kan yakin da Amurka ke yi da Iran
- Donald Trump ya soki shugaban na Gwamnatin Jamus, inda ya caccake shi kan kalaman da ya yi dangane da yakin
- Shugaban kasar na Amurka ya nuna cewa Merz yana tsoma baki a wurin da bai da muhimmanci a gare shi da kuma kasarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake caccakar Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz.
Caccakar da Trump ya yi na zuwa ne yayin da rarrabuwar kai tsakanin Amurka da ɗaya daga cikin manyan ƙawayenta na Turai ke ƙara faɗaɗa saboda sukar da Berlin ke yi wa yaƙin da ake yi da Iran.

Kara karanta wannan
Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya soki Friedrich Merz ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2026.
Me Trump ya ce kan shugaban Jamus?
Shugaban na Amurka ya ba da shawarar cewa ya kamata Merz ya mayar da hankali kan al'amuran Jamus da na Turai maimakon yin tsokaci kan rikicin Gabas Ta Tsakiya.
“Ya kamata shugaban gwamnatin Jamus ya ɓata lokaci mai yawa wajen kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine (inda ya kasance mai rauni sosai!), da gyara ƙasarsa da ta lalace, musamman fannin shige-da-fice da makamashi, maimakon ɓata lokaci wajen tsoma baki ga waɗanda ke kawar da barazanar Nukiliyar Iran."
- Donald Trump
Ya ƙara da cewa yaƙin da ake yi da Iran, wanda ya sa farashin makamashi ya tashi sama a duk faɗin duniya, yana “sa duniya, ciki har da Jamus, ta zama wuri mafi aminci”.
Amurka na sa'insa da kawayenta

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya tuna da mutanen da hare hare suka shafa a Plateau, ya ba da tallafin kudi
Tashar Aljazeera ta ce wannan al’amari ya nuna yadda yaƙin Iran ke raba kan ƙawancen Amurka da Turai, wanda Trump ya ƙaddamar tare da Isra’ila ba tare da tuntuɓar ƙawayen Amurka na NATO ba.
A ranar Laraba, Trump ya ce gwamnatinsa tana nazarin rage yawan dakarun Amurka a Jamus, inda kasancewar sojojin Washington a wurin ake kallonsa a matsayin cibiyar tsaron da take bai wa Turai kariya.
Gwamnatin Berlin ta ce a shirye take don fuskantar yiwuwar rage dakarun Amurka a ƙasarta, yayin da take jaddada haɗin gwiwa da NATO.

Source: Facebook
Me ya hada Trump da Friedrich Merz?
Takaddamar ta samo asali ne lokacin da Merz, wanda a baya yake tare da Amurka da Isra’ila a tsauraran matakan da suke ɗauka kan Iran, ya nuna shakku kan dabarun Washington a cikin rikicin.
Trump ya tsawatawa Merz kan waɗannan kalaman a farkon wannan mako, inda ya ce shugaban na Jamus “bai san abin da yake faɗa ba”.
Shugaban na Amurka yana bayyana yaƙin a matsayin wajibi don hana Iran mallakar makamin nukiliya.
Kudin da Amurka ta kashe a yaki da Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana kudaden da aka kashe yayin yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ma'aikatar tsaron ta ce yaƙin da Amurka ta fafata da Iran ya lakume zunzurutun kuɗi kusan Dala biliyan 25.
Wani babban jami’in ma’aikatar tsaron, Jules Hurst, ne ya tabbatar da hakan ga mambobin majalisar dokokin Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
