Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Ministan Lantarki bayan Adelabu Ya Yi Murabus

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Ministan Lantarki bayan Adelabu Ya Yi Murabus

  • Majalisar Ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta samu sabon Minista biyo bayan nadin da aka yi
  • Mai girma Bola Tinubu ya nada sabon Ministan lantarki wanda zai maye gurbin Adebayo Adelabu sakamakon murabus din da ya yi
  • Shugaba Tinubu ya dauko Joseph Olasunkanmi Tegbe wanda ya fito daga jihar Oyo, ya ba shi mukamin Ministan lantarki na tarayyar Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon Minista wanda zai yi aiki a majalisar ministocinsa.

Shugaba Tinubu ya nada Joseph Olasunkanmi Tegbe a matsayin Ministan lantarki, wanda ke jiran tabbatarwa daga Majalisar dattawa.

Shugaba Tinubu ya nada Mknistan lantarki
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da Joseph Olasunkanmi Tegbe Hoto: @imranmuhdz
Source: UGC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Amurka za ta dauki mummunan mataki kan kasar Najeriya

Tinubu ya nada Ministan lantarki

Bayo Onanuga ya bayyana cewa ana sa ran naɗin zai ƙarfafa gyare-gyaren da ake yi a fannin lantarki, inganta dorewar wutar lantarki a ƙasa, da kuma jawo masu zuba jarin da za su dore.

A cewar Bayo Onanuga, nadin da aka yi wa Tegbe na jiran tantancewa tare da amincewar majalisar dattawan Najeriya.

Wannan naɗi, wanda aka riga aka aika wa Majalisar dattawa domin tantancewa, ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Ministan lantarki, Adebayo Adelabu, wanda ya ajiye aiki domin neman takarar gwamnan Oyo.

Wane ne sabon Ministan lantarki?

Joseph Olasunkanmi Tegbe, ɗan jihar Oyo ne, kuma masanin gyaran tattalin arziƙi da kasafin kuɗi ne wanda yake da gogewar sama da shekaru 30 a fannonin aiki gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

Ya taɓa yin aiki a matsayin shugaban ayyukan a da shawara a kamfanin KPMG na Afirka, inda ya jagoranci tsare-tsaren gyara manufofin kasafin kuɗi, shugabanci, da sauye-sauyen hukumomi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi sauyi a gwamnatinsa, ya nada sababbin ministoci

Joseph Tegbe ya samu gogewa

A halin yanzu, shi ne Babban Darakta kuma mai kula da haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da China, inda yake daidaita ƙoƙarin ci gaba tsakanin ƙasashen biyu.

Tinubu ya nada Joseph Tegbe a matsayin Ministan lantarki
Sabon Ministan lantarki, Joseph Olasunkanmi Tegbe Hoto: @imranmuhdz
Source: Instagram

An kuma bayyana cewa Tegbe yana da gogewa wajen yin aiki a kan gyaran dokoki da hukumomi a fannin lantarki, ciki har da hulɗa da hukumomi irin su hukumar kula da lantarki ta Najeriya (NERC) da kamfanin sayar da lantarki na Najeriya (NBET).

"Shugaban ƙasa yana sa ran cewa Ministan, bayan an tabbatar da shi, zai yi amfani da dumbin iliminsa don ciyar da muhimman gyare-gyare gaba da kuma samar da kyakkyawan sakamako ga 'yan Najeriya a fannin lantarki."

- Bayo Onanuga

Shugaba Tinubu ya nada Ministan harkokin waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ministan da zai kula da ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya.

Shugaba Tinubu ya nada Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin sabuwar Ministar harkokin waje biyo bayan murabus din Yusuf Tuggar.

Hakazalika, shugaban ƙasar ya nada Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin sabon karamin Ministan harkokin waje, wanda ke jiran tantancewar Majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng