Dalilin da Ya Sa Kotun Koli Ta Dage Shari'ar Rikicin Sarautar Kano zuwa Bayan Zaben 2027
- Matakin da Kotun Koli ta dauka na dage sauraron shari’ar sarautar Kano har sai bayan babban zabe ya haifar da ce-ce-ku-ce
- Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Omotayo Yusuf, ya bayyana dalilai masu nasaba da dogon tarihin irin wannan shari'a
- Rikicin sarautar Kano dai na tsakanin Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II da magabacinsa, Aminu Ado Bayero, na ci gaba da daukar hankali
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - A makon jiya ne Kotun Koli ta dage sauraron shari’ar rikicin sarautar jihar Kano zuwa ranar 19 ga watan Afrilu, 2027, watau bayan kammala babban zabe mai zuwa.
Wannan mataki ta haifar da ce-ce-ku-ce tare da jefa shakku a zukatan mutane kan yiwuwar samun katsalandan din siyasa a cikin hukuncin kotun da ak jima ana dako.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta ba Tinubu damar ciyo bashin Dala miliyan 516 daga kasar waje

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta rahoto cewa a zaman da aka yi ranar Litinin, 20 ga Afrilu, 2026, Kotun Koli ta saurari hujjojin farko daga bangarorin da lamarin ya shafa kafin ta sanar da dage shari'ar.
Yadda rikicin sarauta ya faro a Kano
Idan baku manta ba gwamnatin Abdullahi Ganduje ce ta tsige Sarki Muhammadu Sanusi II ta hanyar gyara dokar masarautun Kano amma gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta mayar da shi bayan ta sake yin garambawul ga dokar.
Sai dai Sarkin Kano na 14, Aminu Ado Bayero, wanda Ganduje ya nada Ganduje bayan tsige Sanusi, ya ci gaba da ayyana kansa a matsayin Sarki duk da Gwamna Abba ya sauke shi.
Masu lura da al'amura na ganin akwai siyasa a lamarin musamman yanzu da Abba da Ganduje suke jirgi daya na siyasa, sannan watan Afrilun 2027 wata biyu ne kacal bayan babban zaben kasa.
Dalilin dage shari'ar sarautar Kano
Duk da haka, wani masani, Omotayo Yusuf, ya shaida wa wakilin Legit Hausa a wta hira cewa batun cewa siyasa ce ta sa aka dage shari'ar ba gaskiya ba ne.
A cewarsa, an dage ta ne saboda muhimmancinta da kuma tarihin masarautar Kano a Arewa da ma Najeriya baki daya.
"Ba na jin cewa babban zabe ne ya sa Kotun Koli ta dage shari'ar. Ina ganin cewa (kotun koli) ta yi haka ne saboda yanayin tarihin wannan rikici.
"Masana tarihin sun dade da hasashen cewa kujera mai daraja ta daya kamar Masarautar Kano za ta dauki shekaru ana shari'a kafin a cimma matsaya ta karshe."
"Ba na jin zabe mai zuwa shi ne babban dalili. A maimakon haka, ina ganin saboda yadda wannan kujera take da muhimmanci, za a dauki shekaru ana shari'a.
"Ko da yake ba za a iya cire batun siyasa gaba daya ba, ganin yadda shugabannin siyasa a Kano ke sauya sheka kan wanda suke goyon baya, amma dai za a ja kafa shari'ar har sai an kai ga matsaya ta karshe."
- Omotayo Yusuf.
Lauya ya yi fashin baki kan karar Dan'agundi
A wani labarin, kun ji cewa wani lauya ya bayyana cewa shari’ar Aminu Babba Dan’agundi a Kotun Koli ba ta shafi rikicin sarautar Kano ba da ake ciki.
Bashir Muhammad Tudun Wizirci ya ce karar da Aminu Babba Dan’agundi ya shigar tana tsakaninsa da gwamnatin Kano kawai.
Ya kara da cewa wadanda aka jera a matsayin masu kare kansu sun hada da Majalisar dokokin Kano, ofishin Antoni Janar, da kuma hukumomin tsaro daban-daban.
Asali: Legit.ng

