Tinubu Ya Sallami Shugaban NMDPRA yana tsakiyar Aiki a Kasar Waje, Hotuna Sun Fito

Tinubu Ya Sallami Shugaban NMDPRA yana tsakiyar Aiki a Kasar Waje, Hotuna Sun Fito

  • A jiya Laraba, fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya tsige shugaban hukumar NMDPRA, Sa'idu Mohammed
  • Bayanai sun nuka cewa Tinubu ya sallame shi daga aiki ne a daidai lokacin da ya jagoranci tawagar NMDPRA zuwa wani taro a kasar Jamus
  • Wannan mataki na Tinubu na zuwa ne bayan watanni biyar da nada shi a mukamin shugabancin hukumar da ke kula da harkokin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kori Saidu Mohammed daga mukaminsa na shugaban Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Kasa (NMDPRA).

Rahotannin sun nuna cewa shugaban kasa ya kori shugaban NMDPRA a daidai lokacin da yake kan aikin hukumar a kasar Jamus.

NMDPRA.
Tsohon hugaban hukumar NMDPRA, Saidu Mohammed a taron PTC da ya halarta a kasar Jamus Hoto: NMDPRA_official
Source: Facebook

Shugaban NMDPRA ya halarci taron PTC

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X da karfe 4:05 na yammacin ranar Laraba, ta ce Sa'idu Mohammed ya jagoranci tawagar NMDPRA zuwa taron Pipeline Technology Conference (PTC) a Jamus.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tsige Saidu Mohammed daga shugabancin NMDPRA, ya nada sabon shugaba

An shirya wannan taro na PTC ne a birnin Berlin na kasar Jamus daga ranar 27 zuwa 30 ga Afrilu, 2026, kuma shugaban NMDPRA na cikin wadanda suka halarta daga Najeriya.

Sanarwar ta ce:

“Shugaban mu, Injiniya Saidu Mohammed, ya jagoranci tawagar NMDPRA zuwa taron Pipeline Technology Conference da ake yi a Berlin, Jamus daga 27 zuwa 30 ga Afrilu, 2026.”

Yadda Bola Tinubu ya sallame shi daga aiki

Sai dai bayan kimanin sa’o’i biyu da wallafa wannan sanarwa, Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da cewa Tinubu ya sauke Sa'idu Mohammed daga mukaminsa.

Onanuga ya kuma sanar da cewa Shugaba Tinubu ya nada Rabiu Abdullahi Umar a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Dalilin Tinubu na sauyin shugabanci

An kori Mohammed ne bayan kusan watanni biyar kacal da ya janye shawararsa ta shiga kwamitin gudanarwa na kamfanin Seplat a matsayin darakta mai zaman kansa a watan Disamba 2025, domin ya jagoranci NMDPRA.

Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban hukumar ne bayan murabus din Farouk Ahmed a ranar 17 ga Disamba, 2026, ranar da kamfanin Seplat ya sanar da cewa Mohammed zai shiga kwamitinsa.

Kara karanta wannan

Shaidan sojoji ya fasa kwai a kotu, ya fadi yadda aka shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Bayan wannan gajeren lokaci da ya yi a mukamin, Onanuga ya ce shugaban kasa ya gode masa bisa hidimarsa tare da yi masa fatan alheri a nan gaba.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na sa hannu a Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Manufar Gwamnatin Tinubu

Mai magana da yawun shugaban kasar ya kara da cewa Tinubu na da kudurin tabbatar da ingantaccen shugabanci a muhimman hukumomin da ke kula da harkokin tattalin arziki.

The Cable ta tattaro cewa wannna ba shi ne na farko ba, a watan Nuwamba 2025, Tinubu ya sauke Ogbonnaya Orji daga mukaminsa na shugaban hukumar NEITI a lokacin ya yi wata tafiya zuwa kasashen waje.

Tinubu ya nada sababbin ministoci

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin Ministar harkokin waje ta Najeriya.

Tinubu ya yi wannan nadin ne biyo bayan murabus ɗin Ambasada Yusuf Tuggar, wanda ya ajiye aiki domin shiga takara a zaɓen 2027.

Haka zalika, shugaban ƙasar ya nada Ambasada Sola Enikanolaiye a matsayin sabon karamin Ministan harkokin waje, wanda ke jiran tantancewar Majalisar dattawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262