Kwana Ya Kare: Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jihar Benuwai, Agbgbo Ode Ya Rasu
- An tabbatar da rasuwar shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Benuwai, Dr. Agbgbo Ode a safiyar yau Asabar, 2 ga watan Afrilu, 2026
- Sakatariyar gwamnatin Benuwai, Deborah Aber ta bayyana marigayin a matsayin mutum mai rikon amana, wanda za a dade ba a manta da shi ba
- Ta kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalai, yan uwa da abokan aikin Dr. Ode, tana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga jihar baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, Dakta Agbgbo Ode ya riga mu gidan gaskiya da safiyar yau Asabar.
Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jefa gwamnati da ma'aikata cikin alhini da jimami.

Kara karanta wannan
Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

Source: Facebook
An sanar da rasuwar Dr. Agbgbo Ode
Gwamnatin jihar Benuwai ta tabbatar da rasuwar Dakta Agbgbo Ode, inda ta ce an tabbatar da mutuwarsa ne a safiyar ranar Asabar, 2 ga Mayu, 2026, bayan gajeriyar rashin lafiya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sanarwar rasuwar ta fito ne a cikin wata takarda da sakatariyar gwamnatin jihar Benuwai, Deborah Aber, ta fitar a ranar Asabar.
A cewar sanarwar:
“Cike da bakin ciki da jimami, gwamnatin Benuwai ke sanar da rasuwar Dakta Agbgbo Ode, Shugaban Ma’aikatan gwamnatin jiha.
“Rasuwarsa ta zo ba zato ba tsammani a safiyar ranar Asabar, 2 ga Mayu, 2026, bayan gajeriyar rashin lafiya.”
Gudunmawarsa ga aikin gwamnatin Benuwai
Gwamnatin ta bayyana marigayin a matsayin ginshiki a bangaren aikin gwamnati na jihar, tana mai yabawa da irin kwarewa da gudunmawar da ya bayar ta tsawon lokaci.
Ta kuma bayyana marigayin a matsayin mutum mai rikon amana a duk wani aiki da ya sa a gaba, kuma ya taka muhimmiyar ruwa wajen kawo ci gaba a harkar aikin gwamnati.

Kara karanta wannan
Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027
Sanarwar ta kara da cewa:
“Kwarewarsa da rikon amana a harkokin aikin gwamnati, tare da kokarinsa da basirarsa, sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa aikin gwamnati a jihar, kuma za a dade ba a manta da shi ba,”

Source: Facebook
Gwamnatin Benuwai ta yi ta'aziyya
Har ila yau, gwamnatin Benuwai ta kuma bayyana shi a matsayin gogaggen masani kuma mutum mai mutunci a fagen aikin gwamnati, in ji rahoton da Daily Post ta wallafa.
Sakatariyar gwamnatin ta mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokan aikinsa da daukacin ma’aikatan gwamnatin jihar, tana mai cewa rasuwarsa babbar asara ce ga jihar Benuwai.
Tsohon dan wasan Najeriya ya rasu
A wani labarin na daban, kun ji cewa tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Mike Eneramo ya riga mu gidan gaskiya yayin atisayen motsa jiki a jihar Kaduna.
An ruwaito cewa lamarin ya faru ne da safiya yayin da tsohon dan wasan ya fito atisayen motsa jiki a filin kwallo na makarantar firamare da ke Ungiluwan Yelwa a jihar Kaduna.
Eneramo ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa a shekarar 2018 bayan ya shafe shekaru yana taka leda a ƙasashen waje , musamman a kasar Turkiyya.
Asali: Legit.ng