Dakarun Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Tsageru
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara a yakin da suke yi don tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a jihar Borno bayan sun kai masu harin kwanton bauna yayin da suke tafiya a cikin daji
- Hakazalika, dakarun sojojin sun kwato makamai tare da kayan masarufi daga hannun 'yan ta'addan bayan sun tura su zuwa barzahu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe mutane hudu da ake zargi ’yan ta’adda ne a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai da kayan masarufi yayin wani harin kwanton bauna da suka kai a yankin dajin Sambisa da ke Borno.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sojoji na bataliya ta 21 tare da haɗin gwiwar 'yan sa-kai ne suka gudanar da aikin a safiyar ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilun 2026.
Majiyoyin sun bayyana cewa sojojin sun garzaya wani wurin da ake zargin ’yan ta’addan suna wucewa a yankin “Charlie Five” biyo bayan samun sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan tada ƙayar bayan.
“An yi kicibis da ’yan ta’addan da ke tahowa daga yankin Yale zuwa dajin Sambisa, kuma nan take dakarun suka fafata da su tare da nuna masu bambancin kwarewa."
- Wata majiya
An kwato makamai da kayayyaki
Yayin binciken yankin, an kashe ’yan ta’adda hudu, sannan dakarun sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya tare da harsasai 12 masu kaurin 7.62mm.
Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da buhunan masara niƙaƙƙiya guda biyu da fakitin taliya, waɗanda aka yi amanna suna daga cikin kayan abinci na ’yan ta’addan.
Daga baya tawagar dakarun da suka kai harin kwanton sun koma sansaninsu lafiya ba tare da an samu asarar rai ba, yayin da ake ci gaba da sa-ido da kuma aikin share fage a yankin.

Source: Original
Hukumomin soja sun bayyana cewa yanayin tsaro baki ɗaya a yankin yana cikin kwanciyar hankali, inda dakarun ke ci gaba da kasancewa cikin karsashi da kuzari wajen gudanar da ayyukansu.
Rundunar Operation Hadin Kai tana ci gaba da kai hare-hare da nufin tarwatsa hanyoyin sadarwar ’yan ta’adda da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda sama da 200
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda sama da 200.
Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'addan a sassa daban-daban na Najeriya a cikin watan Afirilun 2026.
DHQ ta bayyana cewa sojojin sun kashe ’yan ta’adda 216 tare da kama wasu mutane 284 da ake zargi, a sassa daban-daban na kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

