Ba Sassauci: Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda Sama da 200
- Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta yi bayani kan nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda
- DHQ ta bayyana cewa sojoji sun hallaka 'yan ta'adda da dama tare da cafke wasu da ake zargi tare da ceto mutanen da aka sace
- Hedkwatar tsaron ta bayyana cewa dakarun sojojin sun samu nasarorin ne a watan Afirilun 2026 a sassa daban-daban na Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da Dakarun sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda.
DHQ ta bayyana cewa dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara a ayyukan da suke gudanarwa a faɗin ƙasar nan a cikin watan Afrilu 2026.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Darakta a fannin yaɗa labaran ayyukan tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2026, a Abuja kan ayyukan sojoji na kowane wata.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Najeriya
Ya bayyana cewa sojojin sun kashe ’yan ta’adda 216 tare da kama wasu mutane 284 da ake zargi, ciki har da manyan shugabannin ƙungiyoyinsu.
Haka kuma, sojojin sun samu nasarar ceto akalla mutane 188 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na kasar nan.
Ya ce dakarun sun kuma ƙwato dumbin makamai da alburusai a cikin wannan lokaci, yayin da suka tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda da mafakar masu aikata laifuffuka da dama.
"A cikin wannan lokaci, rundunonin sojoji sun kashe ’yan ta’adda sama da 200 a fafatawa daban-daban, sun ceto farar hula 188 da aka yi garkuwa da su, da suka haɗa da mata, yara, tsofaffi, manoma, da masu ibada, kuma an mayar da su ga iyalansu."
"Dakarun sun kuma kai samame tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda, mafakar bama-bamai na IED, da wuraren kera makamai ba bisa ƙa’ida ba, yayin da suka kama manyan jagororin ’yan ta’adda, masu kai musu kayan aiki, da masu haɗa baki da su guda 284.”
- Manjo Janar Michael Onoja
Yankunan da aka kashe 'yan ta'adda
Yayin da yake bayar da bayanin yadda ayyukan suka kasance, Onoja ya ce a yankin Arewa maso Gabas, dakarun sun kashe ’yan ta’adda 136, sun kama mutane 144 da ake zargi, sun ceto mutane 18, yayin da wasu ’yan tada ƙayar baya tara suka miƙa wuya.
A Arewa maso Yamma, ya ce dakarun sun kashe ’yan ta’adda 24, sun kama mutane 32 da ake zargi, sun ceto mutane 70, kuma an samu ɗan ta’adda guda ɗaya da ya miƙa wuya.
A Arewa ta Tsakiya, dakarun da ke ƙarƙashin rundunar Operation Savannah Shield sun kashe ’yan ta’adda 21, sun kama mutane 17 da ake zargi, sannan suka ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su.

Source: Twitter
'Yan ta'adda sun sha wuta a hannun sojoji
Hakazalika, dakarun Operation Enduring Peace sun kashe ’yan ta’adda 18, sun kama mutane 48 da ake zargi, sun ceto mutane 53 da aka yi garkuwa da su, yayin da Operation Whirl Stroke suka kashe ’yan ta’adda 14, suka kama mutane 40 da ake zargi, tare da ceto mutane 35.
A yankin Kudu maso Kudu, dakarun Operation Delta Safe sun kama mutane 17 da ake zargi, sun ruguza wuraren tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba guda biyu, sannan suka ƙwato lita 101,443 na man fetur.
A halin da ake ciki kuma, a yankin Kudu maso Gabas, dakarun da ke ƙarƙashin Operation Udo Ka sun kashe ’yan ta’adda uku, sun kama mutane 16 da ake zargi, sannan suka ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a jihar Borno.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda 18 yayin artabu a jihar Borno.
Sojojin sun kuma ƙwato dumbin makamai da alburusai a kusa da gadar Azir da ke yankin Timbuktu da kuma dajin Bulabulin a jihar Borno.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


