Ana dab da zaben gwamna, 'yan sanda sun cafke kwamishina a jihar Osun

Ana dab da zaben gwamna, 'yan sanda sun cafke kwamishina a jihar Osun

  • Rundunar ’yan sandan Osun ta kama Mayowa Adejoorin, kwamishinan muhalli da tsaftar muhalli na jihar, kan harbin da ya faru a wani taron APC a Ilesa ranar Asabar
  • Kamen ya janyo martani daga Imole Campaign Council, wadda ta zargi ’yan sanda da nuna son kai da kuma yi wa kwamishinan zagon siyasa
  • ’Yan sanda sun ce sun kama Adejoorin ne bayan jami’an dabara sun tare wata farar Lexus 350 da ake danganta da lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Jihar Osun - Rundunar ’yan sandan jihar Osun ta kama Mayowa Adejoorin, kwamishinan muhalli da tsaftar muhalli na jihar, kan harbin da ya faru a lokacin wani gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Ilesa ranar Asabar.

Kamen dai ya janyo martani daga Imole Campaign Council, kungiyar yakin neman zaben Gwamna Ademola Adeleke, wadda ta zargi ’yan sanda da nuna son kai tare da cewa ana yi wa kwamishinan hari ne saboda dalilan siyasa.

Kara karanta wannan

Yan APC sun samu raunuka bayan yan daba sun tarwatsa kamfen APC da harbe harbe

'Yan sanda sun cafke kwamishina a Osun
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Osun, Abiodun Ojelabi, ya ce an kama Adejoorin ne bayan jami’ai sun tare wata farar motar Lexus 350 da ake danganta da lamarin.

Yadda harbin ya yaru

Ojelabi ya bayyana cewa harbin ya faru ne bayan an ajiye wata mota mai lambar rajista OSHA04 kusa da wurin da ake gudanar da gangamin APC.

Ya ce wasu mutane da aka bayyana a matsayin jami’an Amotekun sun fito daga motar sannan suka fara harbe-harbe ba tare da nuna inda suke nufi ba, lamarin da ya sa jama’a suka ranta ana kare.

A cewar Ojelabi, wasu magoya bayan APC masu jajircewa sun bi jami’an Amotekun da suka tsere, inda suka kama daya daga cikinsu.

Ya ce wanda aka kama ya zaro wuka tare da kokarin daba wa duk wanda ya matso kusa da shi, kafin daga bisani ya yi amfani da hakan wajen tserewa.

Kara karanta wannan

Ana shirin sauya dan takarar gwamnan PDP a Benue? Gaskiya ta fito

Ojelabi ya ce:

“An gudanar da wani gangami na APC a wasu sassan Ilesa. Ana cikin gangamin sai aka ga wata mota da aka ajiye kusa da su mai lambar OSHA04, sannan wasu mutane da aka bayyana a matsayin jami’an Amotekun suka fito daga motar suka fara harbe-harbe ba tare da nuna inda suke nufi ba, sai kowa ya ranta ana kare."
“Saboda haka wasu jajirtattun mutane daga cikin wadanda ke gudanar da gangamin suka bi wadannan jami’an Amotekun. Wanda suka samu damar kamawa ya zaro wuka ya yi kokarin daba wa duk wanda ya kusanto shi, sannan ya yi amfani da wannan dabarar wajen tserewa.”

An Kama Mutane Biyu

A cewar kakakin ’yan sandan, daga bisani jami’an tsaro sun tare motar Lexus inda suka kama wani jami’in Amotekun da wani mutum da ke cikin motar. Ya ce an kai mutanen biyu hedikwatar rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da bincike.

Ojelabi ya ce binciken farko da aka yi bayan kama su ya nuna cewa mutumin na biyu da ke cikin motar shi ne Kwamishina Mayowa Adejoorin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360

An cafke kwamishina a Osun
Taswirar jihar Osun tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Davido zai kai korafi kan zaben Osun

A wani labarin kuma, kun ji cewa Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya yi gargadi game da zaɓen gwamnan Osun.

Davido ya ce zai nemi taimakon Shugaban Amurka Donald Trump idan ya ga an yi magudi a zaben gwamnan Osun mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com