Manyan Labarai A Yau
An samu barkewar cutar amai da gudawa a wani sansanin 'yan ta'addan ISWAP da ke jihar Borno. Barkewar cutar ta jawo mayaka da dama sun sheka zuwa barzahu.
Hukumar SEMA ta bayyana cewa gwamnatin Jigawa ta fitar da kudaden agajin gaggawa domin tallafawa wadanda ibtila'im guguwa ya shafa a kauyuka 120.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sanya bai da farin jini a wajen ma'aikata. Ya ce bai amincewa a kashe kudi a banza.
An samu tashin wata mummunar gobara a gidan shugaban karamar hukumar Ankpa da ke jihar Kogi. Gobarar ta tashi ne lokacin da iyalansa ke cikin gidan.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi maganar cin nasara a yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Shugaba Trump ya bayyana cewa sun yi nasara.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya karbi shugaban karamar hukuma da ya yi murabus zuwa jam'iyyar ADC. Ya ce jarumai ke komawa ADC.
Batun yan sandan jihohi na daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a taron gwamnoni da sarakunan Arewa da aka gudanar a gidan gwamnatin Kaduna.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana yadda mutumin da ke ikirarin shugabantar hukumar PFIPC, ya yaudare shi suka gana.
Rahotanni daga kafar yada labaram Iran sun nuna cewa akalla sojojin Iran takwasne suka mutu a hare-haren da Amurka ta kai bayan karya yarjejeniya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari