Guguwa Mai Karfi Ta Kashe Mutane, Ta Yi Mummunar Ɓarna a Garuruwa Fiye da 100 a Jigawa

Guguwa Mai Karfi Ta Kashe Mutane, Ta Yi Mummunar Ɓarna a Garuruwa Fiye da 100 a Jigawa

  • Guguwa mai karfin gaske ta rutsa kauyuka da dama a jihar Jigawa, inda ta kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu fiye da 50
  • Rahotanni sun nuna cewa wannan ibtila'in ya shafi gidaje 5,403 a cikin kauyuka 120 da ke kananan hukumomi 13 na jihar Jigawa
  • Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da sakin kudade tallafi cikin gaggawa domin taimakawa wadanda bala'in ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Guguwa mai tsananin karfi ta janyo asarar rayuka da dama a jihar Jigawa, inda aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai tare da jikkata wasu 53 a lokaci guda.

Rahotanni sun nuna cewa guguwar ta yi barna a kauyuka fiye da 100 da ke yankin kananan hukumomi 13 a jihar Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kara karanta wannan

PDP ta yi kaca kaca da gwamnatin Gombe kan zargin bai wa mawakin Kano N315m

Jigawa.
Taswirar jihar Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Premium Times ta ce shugaban Hukumar Bada agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Hannafi Fagam, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli, 2026.

Guguwa ta taɓa kananan hukumomi 13

Bisa bayanan da Fagam ya bayar, ibtila'in guguwar ya rutsa da gidaje 5,403 a kananan hukumomi 13.

Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Dutse, Miga, Gwaram, Birnin Kudu, Ringim, Kiyawa, Babura, Kiri-Kasamma, Buji, Kaugama, Gumel, Gagarawa da Sule-Tankarkar.

Bayanai sun nuna cewa guguwar ta mamaye kauyuka 120 a wadannan kananan hukumomi da aka ambata.

Yadda mutum 7 suka mutu a Jigawa

Dangane da inda mutuwar ta fi yawa, shugaban SEMA ya bayyana cewa karamar hukumar Dutse ce a sahun gaba, inda aka rasa rayukan mutane hudu.

Ya kara da cewa kananan hukumomi uku, wato Miga, Ringim da Sule-Tankarkar, kowannensu ya yi asarar mutum daya.

A cewarsa, makarantu sama da 47 na firamare da sakandare sun lalace, haka kuma asibiti uku da ofisoshin 'yan sanda biyu sun samu matsala, sannan dukiyar jama'a mai dumbin yawa ta salwanta.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

Namadi.
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi yana jawabi a taron rabon kayan tallafi a Dutse Hoto: Umar Namadi
Source: Twitter

Fagam ya kara da cewa gwamnatin jihar ta riga ta amince da sakin kudaden taimako na gaggawa, domin a kai wa wadanda bala'in ya shafa agaji cikin sauri a dukkanin wuraren da abin ya rutsa da su.

Ya kuma yi kira ga kungiyoyin agaji na kasa da kasa, hukumomi na cikin gida, da kuma jama'a baki daya da su hada hannu su taimaka wa wadanda guguwar ta barina wahala.

Mutane sun tafka asara a Jigawa

Wani mazaunin Birnin Kudu, Malam Aminu Aminu Majeh ya tabbatarwa Legit Hausa cewa an yi asarar rayuka da dukiyoyi masu dumbin yawa sakamakon wannan guguwa.

Aminu ya ce da farko hadari aka hada kamar yadda aka saba gani a lokacin damina, amma sai ya zo da iska mai ƙarfi, wacce ta rika rusa gidaje da shagunan jama'a.

"A bayanan da na samu mutum bakwai ne suka mutu, hudu daga ciki a Dutse. Guguwar ta fara ne daga haduwar hadari, inda ta rusa gidaje, kwantenoni da dukiyoyin jama'a," in ji shi.

Kara karanta wannan

An rike dan ta'adda da ya nufi fadar sarki da bindiga zai kai hari

Ana fargabar ambaliya a jihohi 26

A wani labarin, kun ji cewa ma’aikatar muhalli ta tarayya ta yi gargaɗin cewa aƙalla jihohi 26 da Abuja na iya fuskantar ambaliya tsakanin watani Yuni zuwa Yuli, 2026.

Ma'aikatar ta sanar da cewa za a iya samun ambaliyar ne sakamakon hasashen ruwan sama mai ƙarfi a sassan ƙasar nan.

Ta bayyana cewa jihohi 26 da babban birnin tarayya Abuja na cikin yankunan da da za su iya fuskantar babbar ambaliya idan hasashen ya tabbata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262