"Za Mu Rama Sau 20"; Shugaba Trump Ya Yi Sabuwar Barazana ga Iran

"Za Mu Rama Sau 20"; Shugaba Trump Ya Yi Sabuwar Barazana ga Iran

  • Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta riga ta yi nasara a yaƙi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Donald Trump ya yi barazanar cewa duk wani hari da Iran za ta kai zai fuskanci ramuwar gayya sau 20
  • Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya gargadi Amurka cewa duk wanda ya kai hari, shi ma za a kai masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada cewa kasarsa ta riga ta yi nasara a yakin da ake yi da Iran.

Shugaba Trump ya bayyana cewa Iran na son a cimma yarjejeniya bayan sabuwar musayar wutar da aka yi tsakanin kasashen biyu.

Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaba Donald Trump na Amurka a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a cikin jirgin shugaban kasa, Air Force One.

Kara karanta wannan

Iran ta nuna yatsa ga Donald Trump, ta harba makamai kan Kuwait da wasu kasashe 2

Shugaba Donald Trump ya ce Iran ta yi asara sosai a yakin, kuma yanzu tana matukar son cimma yarjejeniya da Amurka.

Sai dai ya nuna shakku kan amincin gwamnatin Iran, inda ya ce:

"Sun rage 'yan kadan sosai, kuma suna matukar son yin yarjejeniya. Amma ban san ko sun cancanci a yi yarjejeniya da su ba. Ban kuma san ko za su mutunta yarjejeniyar ba."

Trump ya yi martani kan hare-haren Iran

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Iran za ta kai hare-hare kan jiragen kasuwanci duk da ikirarinta na son yarjejeniya, Trump ya ce:

"Saboda suna yin abubuwa kamar mahaukata, a gaskiya. Hakan kamar rashin hankali ne. Sun dan fita daga hayyacinsu, amma suna son yarjejeniya matuka."

Shugaban na Amurka ya kuma yi barazanar daukar matakin soja mai tsanani idan Iran ta sake kai hari.

"Mun kai masu mummunan hari. Duk lokacin da suka kai mana hari, za mu rama sau 20."

- Donald Trump

Lokacin da aka tambaye shi ko Amurka na shirin komawa cikakken yakin soja da Iran, Trump ya amsa da cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi wa sojoji ƙarin lbashi mai gwaɓi don inganta walwalarsu a Najeriya

"Ban sani ba. Muna da hanyoyi da dama na samun nasara, amma ta fuskar soja mun riga mun yi nasara."

Ghalibaf ya gargadi kasar Amurka

Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya gargadi Amurka da cewa cin zarafi da karya alkawari ba za su ci gaba da kasancewa ba tare da wani abu ya biyo baya ba.

A wani sako da ya wallafa a shafin X, Ghalibaf ya ce:

"Ina son na bayyana a fili: Idan kuka kai hari, za a kai muku hari."

Mohammad Ghalibaf ya kuma gargadi Amurka game da matsin lambar da take yi kan mashigar ruwa ta Hormuz.

Ghalibaf ya gargadi Amurka
Mohammad Bagher Ghalibaf a cikin jirgin sama Hoto: @MB_Ghalibaf
Source: Twitter

A cewarsa, bude mashigar zai kasance ne bisa tsarin Iran, ba bisa barazanar Amurka ba, inda ya kara da cewa:

"Kada ku ci gaba da wannan yunkuri marar amfani, domin hakan zai kara jefa ku cikin matsala."

Amurka ta kashe sojojin Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun rasa rayukansu bayan hare-haren da Amurka ta kai.

Kara karanta wannan

2027: Fadar shugaban kasa ta yi magana kan barazanar kashe Peter Obi

Gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa sojojin kasar takwas sun rasa rayukansu a sababbin hare-haren da Amurka ta kai Kudancin kasar.

Sojojin da suka mutu sun kasance jami'an rundunar sojin sama da ta ruwa ta Iran sakamakon hare-haren da Amukra ta kai jan biranen Bandar Abbas da Bushehr.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng